Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Labari na 88: Yohanna Ya Yi wa Yesu Baftisma

Labari na 88: Yohanna Ya Yi wa Yesu Baftisma

KA GA kurciyar da take sauka a kan wannan mutumin. Mutumin Yesu ne. Yanzu yana da wajen shekara 30. Kuma mutumin da yake tare da shi Yohanna ne. Mun riga mun koyi wani abu game da shi. Ka tuna sa’ad da Maryamu ta je ta ziyarci ’yar’uwarta Alisabatu, kuma ɗan da yake cikinta ya yi tsalle don murna? Ɗan da ba a haifa ba a lokacin Yohanna ne. Amma menene Yohanna da Yesu suke yi a yanzu?

Baftismar Yesu

Yohanna ya nitsar da Yesu cikin ruwan Kogin Urdun. Haka ake yi wa mutum baftisma. Da farko, za a nisar da shi, sai kuma a fito da shi. Domin wannan ne abin da Yohanna yake yi wa mutane, ake kiransa Yohanna mai Baftisma. Amma me ya sa Yohanna ya yi wa Yesu baftisma?

Yohanna ya yi ne domin Yesu ya zo wurinsa ya ce wa Yohanna ya yi masa baftisma. Yohanna yana yi wa mutane baftisma da suke so su nuna cewa sun tuba daga miyagun abubuwa da suka yi. Amma shin Yesu ya taɓa yin mugun abu ne da zai tuba? A’a, Yesu bai taɓa yin mugun abu ba, domin shi Ɗan Allah ne daga samaniya. Ya ce wa Yohanna ya yi masa baftisma domin wani dalili dabam ne. Bari mu ga dalilin.

Kafin Yesu ya zo wurin Yohanna, shi kafinta ne. Kafinta mai yin kujeru ne da tebura da bencuna na katako. Mijin Maryamu Yusufu kafinta ne, shi ne ya koya wa Yesu aikin kafinta. Amma Jehobah bai aiko da Ɗansa duniya domin ya zama kafinta ba. Yana da aiki na musamman da yake so ya yi, kuma lokaci ya yi da Yesu zai fara wannan aiki. Saboda haka domin ya nuna cewa yanzu ya zo ne ya yi nufin Ubansa, Yesu ya ce Yohanna ya yi masa baftisma. Allah ya yi farin ciki ne da wannan?

Hakika ya yi farin ciki, bayan Yesu ya fito daga cikin ruwan, murya daga sama ta ce: ‘Wannan ɗana ne wanda nake farin ciki da shi.’ Kuma kamar sama ta tsage kuma wannan kurciya ta sauko kan Yesu. Amma ba kurciya ba ce ta gaskiya. Tana dai kama ne da kurciya. Amma ainihi ruhun Allah ne.

Yanzu da abubuwa da yawa da Yesu zai yi tunani a kai, saboda haka ya je wurin da babu kowa ya yi kwanaki 40. A nan ne Shaiɗan ya zo masa. Sau uku Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya sa Yesu ya yi abin da zai sa ya taka dokar Allah. Amma Yesu ya ƙi.

Bayan haka, Yesu ya koma ya sadu da wasu mutane da suka zama mabiyansa na farko ko kuma almajiransa. Sunayensu su ne Andarawus, Bitrus (wanda ana kira Siman), Filibbus da Natanayilu (shi ma a kan kira shi Barthalamawus). Yesu da waɗannan sababbin almajirai suka tafi gundumar Galili. A Galili suka sauka a garinsu Natanayilu wato Kana. A nan Yesu ya je wani babban bikin aure, ya yi kuma mu’ujizarsa ta farko. Ka san ko menene ne? Ya mai da ruwa ya zama giya.

Matta 3:13-17; 4:1-11; 13:55; Markus 6:3; Yohanna 1:29-51; 2:1-12.Tambayoyi

 • Su waye ne waɗannan maza biyu a wannan hoton?
 • Ta yaya ake yi wa mutum baftisma?
 • Su wanene ainihi Yohanna yake wa baftisma?
 • Don wane dalili na musamman ne Yesu ya gaya wa Yohanna ya yi masa baftisma?
 • Ta yaya Allah ya nuna cewa ya yi farin ciki da Yesu ya yi baftisma?
 • Menene ya faru sa’ad da Yesu ya tafi wurin da ba kowa na kwana 40?
 • Su waye ne mabiyan Yesu na farko, ko kuma almajirai, wace mu’ujiza ta farko ne ya yi?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Matta 3:13-17.

  Wane gurbi ne Yesu ya kafa don baftisma na almajiransa? (Zab. 40:7, 8; Mat. 28:19, 20; Luk 3:21, 22)

 • Ka karanta Matta 4:1-11.

  Ta yaya yadda Yesu ya yi amfani da Nassosi da kyau yake ƙarfafa mu mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai? (Mat. 4:5-7; 2 Bit. 3:17, 18; 1Yoh. 4:1)

 • Ka karanta Yohanna 1:29-51.

  Wurin wa Yohanna mai Baftisma ya ja-goranci almajiransa, ta yaya za mu yi koyi da shi a yau? (Yoh. 1:29, 35, 36; 3:30; Mat. 23:10)

 • Ka karanta Yohanna 2:1-12.

  Ta yaya mu’ujizar Yesu na farko ya nuna cewa Jehobah ba ya hana bayinsa kowane abu mai kyau? (Yoh. 2:9, 10; Zab. 84:11; Yaƙ. 1:17)