Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Labari na 99: A Ɗaki a Gidan Sama

Labari na 99: A Ɗaki a Gidan Sama

YANZU daren ranar Alhamis ne, bayan kwana biyu ke nan. Yesu da manzanninsa 12 sun zo cikin wannan babban ɗaki a gidan sama domin su ci abincin bikin Ƙetarewa. Mutumin da kake gani yana fita waje Yahuda Iskariyoti ne. Yana so ya tafi ya gaya wa firistoci yadda za su kama Yesu.

Jibin maraice na Ubangiji

Kwana ɗaya kafin wannan, Yahuda ya tambaye su: ‘Me za ku ba ni idan na taimake ku kuka kama Yesu?’ Suka ce: ‘Sabar azurfa talatin.’ Saboda haka Yahuda zai je ya sami waɗannan mutane saboda ya kai su ga Yesu. Wannan ba mugun abu ba ne?

Sun gama cin abincin bikin Ƙetarewa. Sai Yesu ya fara wani biki kuma na musamman. Ya miƙa wa manzanninsa burodi ya ce: ‘Ku ci, wannan yana nufin jiki na da zan bayar dominku.’ Sai kuma ya ba su kofin inabi ya ce: ‘Ku sha domin wannan yana nufin jini na da za a zubar dominku.’ Littafi Mai Tsarki ya kira wannan ‘jibin maraice na Ubangiji.’

Isra’ila sun ci abincin bikin Ƙetarewa domin ya tuna musu sa’ad da mala’ikan Allah ya ‘ƙetare’ gidajen su a ƙasar Masar, amma ya kashe dukan ɗan farin a gidajen Masarawa. Amma Yesu yana so mabiyansa su tuna da shi, da kuma yadda ya ba da ransa dominsu. Abin da ya sa ke nan ya gaya musu su yi wannan tunawa na musamman kowace shekara.

Bayan sun ci Jibin Maraice na Ubangiji, Yesu ya gaya wa manzanninsa su yi ƙarfin zuciya kuma su kasance da bangaskiya mai ƙarfi. A ƙarshe suka rera waƙar yabo ga Allah kuma suka fita. Dare ya riga ya yi nisa, wataƙila tsakar dare ma ta riga ta wuce. Bari mu ga inda suka je.

Matta 26:14-30; Luka 22:1-39; Yohanna surori 13 zuwa 17; 1 Korinthiyawa 11:20.Tambayoyi

 • Kamar yadda aka nuna a hoto, me ya sa Yesu da manzanninsa 12 suke babban ɗaki a gidan sama?
 • Wane mutum ne yake fita, menene zai yi?
 • Wane abinci na musamman ne Yesu ya soma da aka gama jibin Ƙetarewa?
 • Idin Ƙetarewan ya tuna wa Isra’ilawa game da wane aukuwa ne, kuma menene wannan abinci na musamman ya tuna wa mabiyan Yesu?
 • Bayan Jibin Maraice na Ubangiji, menene Yesu ya gaya wa mabiyansa, kuma menene suka yi?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Matta 26:14-30.

  Ta yaya Matta 26:15 ya nuna cewa Yahuda Iskariyoti ya ci amanar Yesu da ganga?

  Wane manufa biyu ne jinin da Yesu ya zubar ya cika? (Mat. 26:27, 28; Irm. 31:31-33; Afis. 1:7; Ibran. 9:19, 20)

 • Ka karanta Luka 22:1-39.

  A wane azanci ne Shaiɗan ya shiga wurin Yahuda? (Luk 22:3; Yoh. 13:2; A. M. 1:24, 25)

 • Ka karanta Yohanna 13:1-20.

  Domin labarin da ke Yohanna 13:2, Yahuda ya yi laifi ne don abin da ya yi, wane darassi ne bayin Allah za su koya daga wannan? (Far. 4:7; 2 Kor. 2:11; Gal. 6:1; Yaƙ. 1:13, 14)

  Wane darassi ne mai muhimmanci Yesu ya koyar? (Yoh. 13:15; Mat. 23:11; 1 Bit. 2:21)

 • Ka karanta Yohanna 17:1-26.

  A wane azanci ne Yesu ya yi addu’a don mabiyansa su “zama ɗaya”? (Yoh. 17:11, 21-23; Rom. 13:8; 14:19; Kol. 3:14)