Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Labari na 79: Daniel Cikin Ramin Zakuna

Labari na 79: Daniel Cikin Ramin Zakuna

AI YA! AI YA! Kamar dai Daniel yana cikin matsala. Amma kuma zakunan ba su yi masa kome ba! Ka san abin da ya sa? Waye ya saka Daniel cikin wannan rami mai waɗannan zakuna? Bari mu gani.

Sarkin Babila yanzu wani mutum ne mai suna Darius. Yana son Daniel sosai domin Daniel mutumin kirki ne kuma yana da hikima. Darius ya zaɓi Daniel ya zama shugaba a masarautarsa. Wannan ya sa wasu mutane a masarautar suka yi kishin Daniel, ga abin da suka yi

Darius

Suka je wajen Darius suka ce: ‘Mun yarda, ya sarki, cewa ka kafa doka ka ce cikin kwana 30 kada kowa ya yi addu’a ga wani allah ko mutum sai kai kawai, ya sarki. Duk wanda ya ƙi yin biyayya, sai a jefa shi cikin ramin zakuna.’ Darius bai san abin da ya sa waɗannan mutanen suke son a kafa wannan dokar ba. Amma yana gani shawara ce mai kyau, saboda haka ya rubuta dokar. Yanzu ba za a iya canja dokar ba.

Sa’ad da Daniel ya sami labarin dokar, ya tafi gida ya yi addu’a, kamar yadda ya saba. Waɗannan miyagun mutane sun sani cewa Daniel ba zai daina yin addu’a ga Jehobah ba. Suka yi farin ciki domin kamar ƙullin da suka yi su kashe Daniel yana aiki.

Da Sarki Darius ya fahimci dalilin da ya sa waɗannan mutanen suke so a kafa wannan dokar, sai ya yi nadama. Amma ba zai iya canza dokar ba, saboda haka dole ne ya ba da umurni a jefa Daniel cikin ramin zakuna. Amma sarkin ya gaya wa Daniel: ‘Ina fata cewa Allahnka, da kake bauta wa zai cece ka.’

Ran Darius ya ɓaci sosai har ya kasa barci da dare. Washegari ya ruga zuwa ramin zakunan. Ka gan shi a can. Ya yi kira: ‘Daniel, bawan Allah mai rai! Allah da kake bauta wa ya cece ka kuma daga zakuna?’

Daniel cikin ramin zakuna

‘Allah ya aiko da mala’ikansa ya rufe bakin zakuna saboda kada su kashe ni,’ in ji Daniel.

Sarki ya yi farin ciki. Ya ba da umurni a cire Daniel daga cikin ramin. Sai ya sa aka jefa mutanen da suka yi ƙoƙari su kashe Daniel cikin ramin zakunan. Kafin ma su taɓa ƙasa zakunan suka kakkarya ƙasusuwansu.

Sai Sarki Darius ya rubuta zuwa ga dukan mutanen da suke masarautarsa: ‘Na ba da umurni cewa dukan mutane su daraja Allahn Daniel. Ya yi mu’ujiza mai girma. Ya ceci Daniel daga bakin zakuna.’

Daniel 6:1-28.Tambayoyi

 • Wanene Darius, kuma yaya ya ɗauki Daniel?
 • Menene wasu mutane masu kishi suka sa Darius ya yi?
 • Menene Daniel ya yi sa’ad da sami labari game da sabuwar doka?
 • Me ya sa ran Darius ya ɓaci sosai har ya kasa barci, kuma menene ya yi washegari?
 • Ta yaya Daniel ya amsa wa Darius?
 • Menene ya sami miyagun mutane da suka yi ƙoƙari su kashe Daniel, kuma menene Darius ya rubuta wa dukan mutane da suke masarautarsa?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Daniel 6:1-28.

  Ta yaya haɗin baki a kan Daniel ya tuna mana abin da ’yan hamayya suka yi domin su hana aikin Shaidun Jehobah a zamani nan? (Dan. 6:7; Zab. 94:20; Isha. 10:1; Rom. 8:31)

  Ta yaya bayin Allah a yau za su yi koyi da Daniel su kasance masu ‘bin doka?’ (Dan. 6:5, 10; Rom. 13:1; A. M. 5:29)

  Ta yaya za mu yi koyi da misalin Daniel na bauta wa Jehobah “kullum”? (Dan. 6:16, 20; Filib. 3:16; R. Yoh. 7:15)