Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Labari na 72: Allah Ya Taimaki Sarki Hezekiah

Labari na 72: Allah Ya Taimaki Sarki Hezekiah

KA SAN abin da ya sa wannan mutumin yake yi wa Jehobah addu’a? Me ya sa ya baza waɗannan wasiƙun a bagadin Jehobah? Wannan mutumin Hezekiah ne. Shi ne sarkin ƙabilu biyu na kudu na Isra’ila. Kuma ya shiga cikin matsala mai yawa. Me ya sa?

Sarki Hezekiah yana addu’a

Domin sojojin Assuriya sun riga sun halaka ƙabilu 10 na arewa. Jehobah ya ƙyale haka ya faru domin mutanen miyagu ne. Kuma yanzu sojojin Assuriyawan sun zo su yaƙi masarautar ƙabilu biyun.

Sarkin Assuriya ya aika da wasiƙa zuwa ga Sarki Hezekiah. Waɗannan sune wasiƙun da Hezekiah ya baza a gaban Allah. Wasiƙun sun zagi Allah kuma sun ce wa Hezekiah ya ba da gari. Abin da ya sa ke nan Hezekiah yake yin addu’a: ‘Ya Jehobah, ka cece mu daga sarkin Assuriya. Haka zai sa dukan al’ummai su sani cewa kai ne kawai Allah.’ Shin Jehobah zai saurari Hezekiah ne?

Hezekiah sarki ne mai kirki. Shi ba kamar miyagun sarakunan masarautar ƙabilu 10 na Isra’ila ba ne, ko kuma kamar babansa Sarki Ahaz. Hezekiah ya yi ƙoƙari ya bi dukan dokokin Jehobah. Saboda haka, bayan da Hezekiah ya yi addu’a, annabi Ishaya ya aika masa wannan saƙon daga Jehobah: ‘Sarkin Assuriya ba zai shiga cikin Urushalima ba. Babu wani cikin sojojinsa da za su zo ko kusa da ita. Ba za su harba ko kibiya ɗaya ba cikin birnin.”

Ka dubi hoton da ke wannan shafin. Ka san ko su wanene dukan waɗannan sojoji da suka mutu? Assuriyawa ne. Jehobah ya aiki mala’ikansa guda, a cikin dare ɗaya mala’ikan ya kashe sojojin Assuriya 185,000. Saboda haka Sarkin Assuriya ya ba da gari ya koma garinsa.

Mattatun sojojin Assuriya

Aka ceci masarautar ƙabilu biyun, kuma mutanen suka sami salama na ɗan lokaci. Amma bayan Hezekiah ya mutu ɗansa Manasseh ya zama sarki. Manasseh da kuma ɗansa Amon da ya gaje shi dukan su miyagun sarakuna ne. Saboda haka ƙasar ta cika da fin Laifi da kuma mugunta. Sa’ad da bayin Sarki Amon suka kashe shi, ɗansa Josiah ya zama sarkin masarautar ƙabilu biyun.

Sarakuna 18:1-36; 19:1-37; 21:1-25.Tambayoyi

 • Wanene ne wannan mutumin na hoton nan, kuma me ya sa ya damu haka ƙwarai?
 • Waɗanne wasiƙu ne Hezekiah ya ajiye a gaban Allah, kuma menene Hezekiah yake addu’a a kai?
 • Wane irin sarki ne sarki Hezekiah, kuma wane saƙo ne Jehobah ya aika masa ta bakin annabi Ishaya?
 • Menene mala’ikan Allah ya yi wa Assuriyawa, kamar yadda aka nuna a wannan hoton?
 • Ko da yake masarautar ƙabilu biyu sun sami salama na ɗan lokaci, menene ya faru bayan Hezekiah ya mutu?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta 2 Sarakuna 18:1-36.

  Ta yaya ne kakakin Assuriyawa Rabshakeh ya yi ƙoƙarin ya raunana bangaskiyar Isra’ilawa? (2 Sar. 18:19, 21; Fit. 5:2; Zab. 64:3)

  Ta yaya Shaidun Jehobah suke bin misalin Hezekiah sa’ad da suke bi da ’yan hamayya? (2 Sarakuna 18:36; Zabura 39:1; Misalai 26:4; 2 Timothawus 2:24)

 • Ka karanta 2 Sarakuna 19:1-37.

  Ta yaya mutanen Jehobah a yau suke koyi da Hezekiah a lokacin masifa? (2 Sar. 19:1, 2; Mis. 3:5, 6; Ibran. 10:24, 25; Yaƙ. 5:14, 15)

  Waɗanne nasarori uku ne aka yi a kan Sennacherib, kuma ya bi misalin wanene a annabce? (2 Sar. 19:32, 35, 37; R. Yoh. 20:2, 3)

 • Ka karanta 2 Sarakuna 21:1-6, 16.

  Me ya sa za a iya cewa Manasseh yana ɗaya daga cikin miyagun sarakuna da suka yi sarauta a Urushalima? (2 Laba. 33: 4-6, 9)