Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Labari na 64: Sulemanu Ya Gina haikali

Labari na 64: Sulemanu Ya Gina haikali

KAFIN Dauda ya mutu, ya ba wa Sulemanu zanen da Allah ya ba shi na haikali. A shekararsa ta huɗu a kan gadon sarauta, Sulemanu ya fara gina haikalin, kuma ya ɗauki shekara bakwai da rabi kafin ya gama. Mutane dubbai suka yi aikin gina haikalin, kuma ginin ya ci kuɗi mai yawa. Domin an yi amfani da zinariya da azurfa masu yawa.

Haikalin yana da ɗakuna biyu, kamar yadda mazauni yake da shi. Amma waɗannan ɗakunan sun yi biyun na mazauni. Sulemanu ya sa aka saka akwatin alkawari a cikin ɗaki na ciki na haikalin, kuma wasu abubuwa da aka ajiye a mazauni aka saka su a cikin ɗaya ɗakin.

Sa’ad da aka gama gina haikalin aka yi gagarumin biki. Sulemanu ya durƙusa a gaban haikalin ya yi addu’a, kamar yadda kake gani a wannan hoton. ‘Sammai ma ba su da girman da za su ɗauke ka,’ Sulemanu ya gaya wa Jehobah, ‘balle a ce wannan haikali ya ɗauke ka. Amma Ya, Allahna, ka saurari mutanenka sa’ad da suka fuskanci nan suka yi addu’a.’

Sarki Sulemanu yana addu’a

Sa’ad da Sulemanu ya gama addu’arsa, wuta ta sauko daga sama. Ta ƙone dukan hadaya na dabbobi da ya yi. Kuma haske daga Jehobah ya cika haikalin. Wannan ya nuna cewa Jehobah yana sauraro, kuma ya yi farin ciki da haikalin da kuma addu’ar Sulemanu. Mutane suka soma zuwa bauta a haikalin maimakon a mazauni.

Sulemanu ya yi sarauta cikin hikima na dogon lokaci, kuma mutane suka yi farin ciki. Amma Sulemanu ya auri mata da yawa daga wasu ƙasashe da ba sa bauta wa Jehobah. Ka ga ɗaya daga cikinsu tana bauta wa gunki? A ƙarshe waɗannan mata suka sa Sulemanu ya bauta wa wasu alloli shi ma. Ka san abin da ya faru sa’ad da Sulemanu ya yi haka? Bai mallaki mutanen ta hanyar kirki ba. Ya zama mai cin zali kuma mutane ba su yi farin ciki ba.

Sarki Sulemanu yana bauta wa gunki

Wannan ya sa Jehobah ya yi fushi da Sulemanu, ya gaya masa: ‘Zan ƙwace mulkin daga gare ka in ba wa wani mutum dabam. Ba zan yi haka ba sa’ad da kake da rai, amma sa’ad da ɗanka yake sarauta. Amma ba zan karɓe dukan mutanen masarautar daga hannun ɗanka ba.’ Bari mu ga abin da ya faru.

1 Labarbaru 28:9-21; 29:1-9; 1 Sarakuna 5:1-18; 2 Labarbaru 6:12-42; 7:1-5; 1 Sarakuna 11:9-13.Tambayoyi

 • Tsawon wane lokaci ne ya ɗauki Sulemanu don ya gama gina haikalin Jehobah, kuma me ya sa ginin ya yi tsada sosai?
 • Ɗakuna nawa ne ke cikin haikalin, kuma me aka sa cikin ɗakuna na ciki?
 • Menene Sulemanu ya ce a addu’arsa sa’ad da aka gama haikalin?
 • Ta yaya Jehobah ya nuna cewa yana farin ciki da addu’ar Sulemanu?
 • Menene matan Sulemanu suka sa ya yi, kuma me ya faru da Sulemanu?
 • Me ya sa Jehobah ya yi fushi da Sulemanu, menene Jehobah ya ce masa?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta 1 Labarbaru 28:9, 10.

  Domin kalmomin Dauda da aka rubuta a 1 Labarbaru 28:9, 10, me ya kamata mu yi ƙoƙari mu riƙa yi a rayuwarmu ta yau da kullum? (Zab. 19:14; Filib. 4:8, 9)

 • Ka karanta 2 Labarbaru 6:12-21, 32-42.

  Ta yaya Sulemanu ya nuna cewa ba ginin da ’yan adam suka yi da zai iya ɗaukan Allah Maɗaukaki? (2 Laba. 6:18; A. M. 17:24, 25)

  Menene kalmomin Sulemanu da ke 2 Labarbaru 6:32, 33 suka nuna game da Jehobah? (A. M. 10:34, 35; Gal. 2:6)

 • Ka karanta 2 Labarbaru 7:1-5.

  Yadda ’ya’yan Isra’ila suka motsa su yi furci na yabo ga Jehobah sa’ad da suka ga ɗaukakarsa, ta yaya yin tunani game da albarkar Jehobah a kan mutanensa ya kamata ya shafe mu a yau? (2 Laba. 7:3; Zab. 22:22; 34:1; 96:2)

 • Ka karanta 1 Sarakuna 11:9-13.

  Ta yaya ne tafarkin rayuwar Sulemanu ya nuna muhimmancin kasancewa da aminci har zuwa ƙarshe? (1 Sar. 11:4, 9; Mat. 10:22; R. Yoh. 2:10)