Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Labari na 7: Gwarzon Mutum

Labari na 7: Gwarzon Mutum
Ahnuhu

SA’AD da mutane suka fara yawa a duniya, yawancinsu sun yi miyagun abubuwa kamar Kayinu. Amma akwai mutum ɗaya da ya bambanta. Shi ne wannan mutumin mai suna Ahnuhu. Ahnuhu gwarzon mutumi ne. Dukan mutane da suke tare da shi suna yin miyagun abubuwa, duk da haka Ahnuhu ya ci gaba da bauta wa Allah.

Ka san abin da ya sa mutanen suka yi ta yin miyagun abubuwa? Ka tuna, wanene ya sa Adamu da Hauwa’u suka yi rashin biyayya ga Allah ta wajen cin ’ya’yan itace da Allah ya ce kada su ci? Hakika, wani mugun mala’ika ne. Littafi Mai Tsarki ya kira shi Shaiɗan. Yana ƙoƙari kuma ya sa kowa ya yi mugun abu.

Fashi da kisa

Wata rana Jehobah ya sa Ahnuhu ya gaya wa mutanen abin da ba sa so su ji. Ga abin da ya ce: ‘Allah za ya halaka masu mugunta wata rana.’ Wataƙila mutanen sun yi fushi sosai da suka ji haka. Wataƙila ma sun yi ƙoƙari su kashe Ahnuhu. Saboda haka, Ahnuhu yana bukatar ya kasance da ƙarfin zuciya domin ya gaya wa mutanen abin da Allah zai musu.

Allah bai ƙyalle Ahnuhu ya daɗe sosai a tsakanin waɗannan mutane masu mugunta ba. Shekara 365 kawai ya yi. Me ya sa muka ce “shekara 365 kawai”? Domin mutane a wancan zamani suna rayuwa mai tsawo fiye da zamanin nan. Ɗan Ahnuhu Me·thu′se·lah ya yi shekara 969 a duniya!

Mutane suna mugunta

Bayan da Ahnuhu ya mutu, muguntar mutane ta ci gaba ƙwarai. Domin Littafi Mai Tsarki ya ce ‘mugunta kawai suke tunaninsa a dukan lokaci,’ kuma ya ce ‘duniya ta cika da mugunta.’

Ka san abin da ya sa duniya ta cika da damuwa a wancan zamanin? Domin Shaiɗan ya sami wata sabuwar hanyar sa mutane su yi mugun abu ne. Za mu koyi game da wannan a gaba.

Farawa 5:21-24, 27; 6:5; Ibraniyawa 11:5; Yahuda 14, 15.Tambayoyi

 • Ta yaya Ahnuhu ya bambanta?
 • Me ya sa mutane a zamanin Ahnuhu suke ta yin miyagun abubuwa?
 • Waɗanne miyagun abubuwa ne mutane suke yi? (Dubi hoto.)
 • Me ya sa Ahnuhu yake bukatar ya kasance da ƙarfin zuciya?
 • Shekara nawa ne mutane suke yi a wancan zamanin, kuma shekara nawa Ahnuhu ya yi?
 • Menene ya faru bayan Ahnuhu ya mutu?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Farawa 5:24, 27.

  Wane irin dangantaka ce Ahnuhu ya yi da Jehobah? (Far. 5:24)

  In ji Littafi Mai Tsarki, wane mutum ne ya fi kowa tsufa a duniya, kuma shekarunsa nawa ne sa’ad da ya mutu? (Far. 5:27)

 • Ka karanta Farawa 6:5.

  Yaya yanayi ya zama a duniya bayan mutuwar Ahnuhu, kuma yaya wannan ya yi kama da zamaninmu? (2 Tim. 3:13)

 • Ka karanta Ibraniyawa 11:5.

  Wane halin Ahnuhu ne ya ‘game Allah sarai’ kuma menene sakamakon haka? (Far. 5:22)

 • Ka karanta Yahuda 14, 15.

  Ta yaya Kiristoci a yau za su yi koyi da ƙarfin zuciyar Ahnuhu, sa’ad da suke yi wa mutane gargaɗi game da yaƙin Armagedon mai zuwa? (2 Tim. 4:2; Ibra. 13:6)