Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Labari na 10: Ruwan Tufana Mai Yawa

Labari na 10: Ruwan Tufana Mai Yawa

A WAJE da jirgin, mutane suka ci gaba da ayyukansu na yau da kullum kamar dā. Domin har yanzu ba su yarda cewa za a yi ruwan Tufana ba. Wataƙila sun yi ta dariya fiye da dā. Amma ba da daɗewa ba suka daina dariya.

Ambaliyar ruwa ta kewaye mutane da dabbobi da suka tsorata

Farat ɗaya ruwa ya fara malalowa. Ruwa ya malalo daga sama kamar yadda kake zubar da ruwa da bokiti. Gaskiya Nuhu ya faɗa! Amma babu wanda zai iya shiga jirgin kuma domin sun riga sun makara. Jehobah ya riga ya rufe ƙofar da kyau.

Ba da daɗewa ba ruwa ya cika ko’ina. Ruwan ya zama kamar babban kogi. Yana tuge itatuwa yana ture manyan duwatsu, kuma yana ta ƙara. Mutanen suka tsorata. Suka hau kan tudu. Ina, suna da sun saurari Nuhu sun shiga cikin jirgin sa’ad da ƙofar take buɗe! Amma yanzu sun riga sun makara.

Ruwan ya ci gaba da ƙaruwa. Ruwa ya yi ta zubowa daga sama dare da rana har kwana 40. Ya yi ta ƙaruwa ba daɗewa ba ya rufe dutse da ya yi tsawo. Kamar yadda Allah ya ce, dukan mutane da kuma dabbobi da suke waje suka mutu. Amma dukan waɗanda suke cikin jirgin suka tsira.

Nuhu da ’ya’yansa sun yi aiki mai kyau wajen gina jirgin. Ruwan ya ɗaga shi sama, yana yawo a kan ruwan. Wata rana bayan da aka daina ruwa, rana ta fito. Abin sha’awa! Ko’ina babu kome sai ruwa. Abin da ake gani kawai sai jirgin yana yawo a kan ruwan.

Jirgin yana yawo a kan ruwa

Ƙattan duka sun mutu. Ba su ƙara zaluntar mutane ba kuma. Dukansu sun mutu tare da uwayensu da sauran miyagun mutane. To, me ya sami ubanninsu?

Ubannin ƙattan ba mutane ba ne kamarmu. Mala’iku ne da suka sauko daga sama su zauna kamar mutane a duniya. Saboda haka, sa’ad da Tufana ta zo, ba su mutu ba tare da sauran mutanen. Suka bar jikin mutane da suka yi wa kansu, suka koma mala’iku suka koma sama. Amma ba a ƙyale su ba su shiga tsakanin iyalin mala’iku na Allah. Saboda haka suka zama mala’ikun Shaiɗan. A cikin Littafi Mai Tsarki ana kiransu aljanu.

Sai Allah ya sa iska ta busa, ruwan tufana ya fara bushewa. Bayan wata biyar jirgin ya sauka a kan dutse. Bayan wasu kwanaki da yawa, waɗanda suke cikin jirgin suna iya ganin tsololon duwatsun. Ruwan ya ci gaba da bushewa.

Sai Nuhu ya saki baƙar tsuntsuwa da ake kira hankaka daga cikin jirgin. Sai ta yi yawo na ɗan lokaci ta sake dawowa, domin babu inda za ta sauka. Ta ci gaba da yin haka idan ta koma sai ta sauka a kan jirgin.

Kurciya

Nuhu yana so ya gani ko ruwan ya bushe daga duniya, sai ya saki kurciya ta fita daga jirgin. Kurciyar ma ta koma domin ba ta sami wurin da za ta sauka ba. Nuhu ya sake sakan kurciyar, sai ta koma da ganyen zaitun a bakinta. Saboda haka, Nuhu ya sani cewa ruwan ya ragu. Nuhu ya sake sakan kurciyar kuma sai ta sami busashen wuri ta zauna.

Sai Allah ya yi wa Nuhu magana. Ya ce: ‘Ka fita daga jirgin. Tare da iyalinka da kuma dabbobin.’ Sun yi fiye da shekara guda a cikin jirgin. Muna iya tunanin farin cikinsu sa’ad da suka fito daga cikin jirgin da ransu!

Farawa 7:10-24; 8:1-17; 1 Bitrus 3:19, 20.Tambayoyi

 • Me ya sa babu wanda zai iya shiga cikin jirgin da zarar an fara ruwa?
 • Jehobah ya sa an yi ruwa na kwana nawa, kuma yaya zurfin ruwan ya zama?
 • Menene ya sami jirgin sa’ad da ruwan ya fara rufe duniya?
 • Ƙattan su tsira ne daga Tufana, kuma menene ya faru da iyayen ƙattan?
 • Menene ya faru da jirgin bayan watanni biyar?
 • Me ya sa Nuhu ya saki hankaka daga cikin jirgin?
 • Ta yaya Nuhu ya sani cewa ruwa ya ragu daga duniya?
 • Menene Allah ya gaya wa Nuhu bayan shi da iyalinsa sun yi fiye da shekara guda cikin jirgin?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Farawa 7:10-24.

  Dukan abubuwa masu rai ne aka halaka daga duniya? (Far. 7:23)

  Kwanaki nawa aka yi kafin ruwan Tufana ya ragu? (Far. 7:24)

 • Ka karanta Farawa 8:1-17.

  Ta yaya Farawa 8:17 ta nuna cewa ainihin nufin Jehobah ga duniya bai canja ba? (Far. 8:17; 1:22)

 • Ka karanta 1 Bitrus 3:19, 20.

  Sa’ad da mala’iku da suka yi tawaye suka koma sama wane hukunci aka yi musu? (Yahuda 6)

  Ta yaya labarin Nuhu da iyalinsa ya ƙarfafa dogararmu ga iyawar Jehobah ya ceci mutanensa? (2 Bit. 2:9)