Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Labari na 6: Ɗan Kirki, da Kuma Mugun Ɗa

Labari na 6: Ɗan Kirki, da Kuma Mugun Ɗa

KA GA Kayinu da Habila a nan. Dukansu sun girma. Kayinu ya zama manomi. Yana noman hatsi da ’ya’yan itatuwa da kuma kayan lambu.

Kayinu da Habila suna haɗaya ga Allah

Habila kuma ya zama makiyayin tumaki. Yana jin daɗin kula da ’yan tumaki. Suna girma su zama manyan tumaki, saboda haka, ba da daɗewa ba tumakin Habila suka yi yawa.

Wata rana sai Kayinu da Habila suka so su yi wa Allah baiko. Kayinu ya kawo wasu abubuwa da ya nome. Habila kuwa ya kawo kyakkyawa cikin tumakinsa. Jehobah ya yi farin ciki da Habila da kuma baikonsa. Amma bai yi farin ciki ba da Kayinu da kuma baikonsa. Ka san abin da ya sa?

Ba domin baikon Habila ya fi na Kayinu kyau ba ne. Amma domin Habila mutumin kirki ne. Yana ƙaunar Jehobah da kuma ɗan’uwansa. Amma Kayinu mugu ne; ba ya ƙaunar ɗan’uwansa.

Saboda haka, Allah ya gaya wa Kayinu ya canja halinsa. Amma Kayinu ya ƙi. Ya cika da fushi domin Allah yana son Habila fiye da shi. Saboda haka, Kayinu ya ce wa Habila, ‘Bari mu fita yawo.’ A can inda babu kowa, Kayinu ya bugi Habila ɗan’uwansa. Ya buge shi da ƙarfi sosai, ya kashe shi. Wannan ba mugun abu ba ne da Kayinu ya yi?

Kayinu yana tserewa bayan ya kashe Habila

Ko da yake Habila ya mutu, Allah bai manta da shi ba. Habila mutumin kirki ne, kuma Jehobah ba ya manta irin waɗannan mutanen. Saboda haka, wata rana Jehobah Allah zai dawo da Habila zuwa rai. A wannan lokaci Habila ba zai sake mutuwa ba. Zai rayu a nan duniya har abada. Ba za ka so ka san Habila ba?

Amma Allah ba ya farin ciki da mutane kamar su Kayinu. Saboda haka, bayan Kayinu ya kashe ɗan’uwansa, Allah ya yi masa horo, ya kore shi daga sauran iyalinsa. Sa’ad da Kayinu ya koma da zama a wani ɓangare na duniya, ya ɗauki ƙanwarsa, ta zama matarsa.

Sai Kayinu da matarsa suka fara haihuwa. Wasu ’ya’yan Adamu da Hauwa’u suka auri juna, su ma suka haifi ’ya’ya. Ba da daɗewa ba mutane suka yi yawa a duniya. Bari mu koyi game da wasunsu.

Farawa 4:2-26; 1 Yohanna 3:11, 12; Yohanna 11:25.Tambayoyi

 • Wace sana’a ce Kayinu da Habila suka shiga?
 • Wane baiko Kayinu da Habila suka bai wa Jehobah?
 • Me ya sa Jehobah ya yi farin ciki da baikon Habila, kuma me ya sa bai yi farin ciki ba da na Kayinu ba?
 • Wane irin mutumi ne Kayinu, kuma ta yaya Jehobah ya so ya yi masa gyara?
 • Menene Kayinu ya yi sa’ad shi da ƙaninsa kaɗai suke daji?
 • Ka bayyana abin da ya faru da Kayinu bayan ya kashe ɗan’uwansa.

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Farawa 4:2-26.

  Ta yaya Jehobah ya kwatanta mugun yanayin da Kayinu ya shiga? (Far. 4:7)

  Ta yaya Kayinu ya nuna abin da ke cikin zuciyarsa? (Far. 4:9)

  Menene ra’ayin Jehobah game da zubar da jinin marar laifi? (Far. 4:10; Ish. 26:21)

 • Ka karanta Farawa 1 Yohanna 3:11, 12.

  Me ya sa Kayinu ya yi fushi ƙwarai, kuma ta yaya wannan ya kasance gargaɗi a gare mu a yau? (Far. 4:4, 5; Mis. 14:30; 28:22)

  Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ko idan dukan iyalanmu suka yi hamayya da Jehobah, mu za mu iya kasancewa da aminci? (Zab. 27:10; Mat.10:21, 22)

 • Ka karanta Yohanna 11:25.

  Wane tabbaci ne Jehobah ya bayar game da dukan waɗanda suka mutu domin adalci? (Yoh. 5:24)