Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Labari na 114: Ƙarshen Dukan Mugunta

Labari na 114: Ƙarshen Dukan Mugunta

ME KAKE gani a nan? Hakika, sojoji a kan fararen dawakai. Amma ka lura da inda suka fito. Waɗannan dawakai suna fitowa ne daga sama! Amma da gaske ne akwai dawakai a sama?

Yesu a matsayin Sarki a sama

A’a, waɗannan ba dawakai ba ne na gaskiya. Mun san haka domin dawakai ba sa gudu a cikin gajimari, za su iya ne? Amma Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da dawakai a sama. Ka san abin da ya sa ya yi haka?

Domin a dā ana amfani da dawakai sosai wajen yaƙe-yaƙe. Saboda haka Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah zai yi yaƙi da mutane a duniya ta yin maganar mutane a kan dawakai suna zuwa daga sama. Ka san sunan wurin da za a yi wannan yaƙin? Armagedon. Wannan yaƙin domin a halaka dukan mugunta ne daga duniya.

Yesu ne zai yi ja-gora a wannan yaƙin na Armagedon. Ka tuna, Yesu ne Jehobah ya zaɓa ya zama sarkin gwamnatinsa. Abin da ya sa ke nan Yesu ya saka rawanin sarauta. Takobin kuma ya nuna cewa zai halaka dukan abokan gaban Allah. Ya kamata ne mu yi mamakin cewa Allah zai halaka dukan miyagun mutane?

Ka dubi Labari na 10. Me ka gani a can? Tufana da ta halaka miyagun mutane. Waye ya kawo wannan Tufana? Jehobah Allah ne. Dubi labari na 15. Menene yake faruwa a nan? Jehobah ya halaka Saduma da Gwamarata da wuta.

Ka juya zuwa Labari na 33. Ka dubi abin da yake faruwa da karusa da dawakai na Masarawa. Waye ya sa ruwa ya halaka su? Jehobah ne. Ya yi haka ne domin ya kāre mutanensa. Ka dubi Labari na 76. Jehobah ya ƙyale a halaka mutanensa Isra’ilawa domin muguntarsu.

Saboda haka kada mu yi mamakin cewa Jehobah zai aiko da sojojinsa na samaniya su halaka dukan mugunta a duniya. Ka yi tunanin abin da wannan yake nufi! Ka juya zuwa shafi na gaba.

Ru’ya ta Yohanna 16:16; 19:11-16.Tambayoyi

 • Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya yi maganar dawakai a sama?
 • Menene sunan yaƙin Allah da mugaye a duniya, menene manufar wannan yaƙin?
 • Daga wannan hoton, wanene zai shugabancin yaƙin, me ya sa ya saka kambi, menene takobinsa yake nufi?
 • Bisa ga abin da aka tattauna a Labarai na 10 da 15, me ya sa bai kamata mu yi mamaki ba cewa Allah zai halaka mugayen mutane?
 • Ta yaya Labari na 33, 36, da 76 suka nuna mana cewa Allah zai halaka mugaye ko idan suna da’awa suna bauta masa?

Ƙarin tambayoyi

 • Ta yaya Nassosi ya bayana sarai cewa Yesu Kristi shi ne matuƙin farin doki? (R. Yoh. 1:5; 3:14; 19:11; Isha. 11:4)

  Ta yaya jini da aka yafa a tufar Yesu ya tabbatar cewa zai gama cin nasara? (R. Yoh. 14:18-20; 19:13; Isha. 63:1-6)

  Su wanene wataƙila za a haɗa cikin rundunar da suka bi Yesu a farin dokinsa? (R. Yoh. 12:7; 19:14; Mat. 25:31, 32)

  Ta yaya Nassosi ya bayana sarai cewa Yesu Kristi shi ne matuƙin farin doki? (R. Yoh. 1:5; 3:14; 19:11; Isha. 11:4)