Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Sashe na 7: Daga Tashin Yesu a Matattu Zuwa Ɗaurin Bulus a Kurkuku

Sashe na 7: Daga Tashin Yesu a Matattu Zuwa Ɗaurin Bulus a Kurkuku

A kwana na uku bayan mutuwarsa, an ta da Yesu daga matattu. A wannan ranar ya bayyana wajen sau biyar ga mabiyansa a lokatai dabam dabam. Yesu ya ci gaba da bayyana musu har kwana 40. Bayan haka, sa’ad da wasu almajiransa suke kallo, Yesu ya tashi sama. Bayan kwana goma Allah ya zubo da ruhu mai tsarki ga mabiyan Yesu da ke Urushalima.

Daga baya abokan gaban Allah suka jefa manzannin a kurkuku, amma mala’ika ya fitar da su. ’Yan hamayya suka jejjefi almajiri Istafanus suka kashe shi. Za mu ga yadda Yesu ya zaɓi ɗaya daga cikin waɗannan ’yan hamayya ya zama bawansa na musamman, kuma shi ne ya zama manzo Bulus. Bayan shekara uku da rabi da mutuwar Yesu, Allah ya aiki manzo Bulus ya yi wa’azi ga Karniliyus da iyalinsa wanda ba Yahudawa ba ne.

Bayan wajen kamar shekara 13 Bulus ya yi tafiyarsa ta farko ta wa’azi. A tafiyarsa ta biyu Timothawus ya bi shi. Za mu koyi yadda Bulus da abokan tafiyarsa suka yi farin ciki wajen bautar Allah. A ƙarshe aka jefa Bulus a kurkuku a Roma. Bayan shekara biyu an sallame shi, amma kuma aka sake jefa shi kurkuku kuma aka kashe shi. Abubuwan da suka faru a SASHE NA 7 sun faru ne cikin shekaru 32.

 Haske ya makantar da Shawulu