Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Labari na 35: Jehobah Ya Ba da Dokokinsa

Labari na 35: Jehobah Ya Ba da Dokokinsa

BAYAN kamar watanni biyu da barin ƙasar Masar, Isra’ilawa suka isa Dutsen Sinai, da ake kuma kira Horeb. A wannan wurin ne Jehobah ya yi magana da Musa daga kurmi mai cin wuta. Mutane suka yi zango a nan na ɗan lokaci.

Sa’ad da mutanen suke jira a ƙarƙashin dutsen, Musa ya hau dutsen. A kan dutsen Jehobah ya gaya wa Musa yana son Isra’ilawa su yi masa biyayya kuma su zama mutanensa na musamman. Sa’ad da Musa ya sauko, ya gaya wa Isra’ilawan abin da Jehobah ya ce. Kuma mutanen suka ce za su yi wa Jehobah biyayya, domin suna so su zama mutanensa.

Sai Jehobah ya yi wani abin mamaki. Ya sa saman dutsen ya fara hayaki, ya kuma sa aradu ya yi ta ƙara. Kuma ya yi wa mutanen magana: ‘Ni ne Jehobah Allahnku ni na fito da ku daga ƙasar Masar.’ Sai ya ba da doka: ‘Kada ku bauta wa wasu alloli sai ni kaɗai.’

Allunan dutse guda biyu

Allah ya ba wa Isra’ilawan wasu ƙarin dokoki tara. Mutanen suka tsorata ƙwarai. Suka gaya wa Musa: ‘Kai ka yi mana magana domin muna tsoro idan Allah ya yi mana magana za mu mutu.’

Daga baya Jehobah ya gaya wa Musa: ‘Ka zo gare ni a kan dutsen. Zan kuma ba ka alluna biyu na dutse waɗanda zan rubuta dokokin da nake so mutanen su kiyaye su.’ Sai Musa ya sake zuwa kan dutsen. Ya yi kwana 40 a kan dutsen.

Allah yana da dokoki masu yawa domin mutanensa. Musa ya rubuta waɗannan dokoki. Allah kuma ya ba wa Musa allunan dutse guda biyu. A kan waɗannan, Allah da kansa ya rubuta dokoki 10 da ya gaya wa mutanen. Kuma ana kiransu Dokoki Goma.

Musa a Dutsen Sinai

Dokokin Goman dokoki ne masu muhimmanci. Haka nan kuma sauran dokokin da Allah ya ba wa Isra’ilawa. Ɗaya daga cikin waɗannan dokokin ta ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka.’ Wata kuma ta ce: “Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.’ Yesu Kristi, Ɗan Allah ya ce waɗannan biyu sune dokoki mafiya girma da Jehobah ya ba mutanen Isra’ila. A nan gaba za mu koyi abubuwa da yawa game da Ɗan Allah da kuma koyarwansa.

Fitowa 19:1-25; 20:1-21; 24:12-18; 31:18; Kubawar Shari’a 6:4-6; Leviticus 19:18; Matta 22:36-40.Tambayoyi

 • Bayan kamar wata biyu da barin ƙasar Masar, a ina ne Isra’ilawa suka yi zango?
 • Menene Jehobah ya ce yake so mutanen su yi, kuma yaya suka amsa?
 • Me ya sa Jehobah ya ba Musa allunan dutse gida biyu?
 • Ban da Dokoki goman, waɗanne dokoki ne kuma Jehobah ya ba wa Isra’ilawa?
 • Waɗanne dokoki biyu ne Yesu Kristi ya ce su ne mafiya girma?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Fitowa 19:1-25; 20:1-21; 24:12-18 da kuma 31:18.

  Ta yaya kalmomin da suke rubuce a Fitowa 19:8 suka taimake mu mu fahimci abin da keɓe kai na Kirista ya ƙunsa? (Mat. 16:24; 1 Bit. 4:1-3)

 • Ka karanta Kubawar Shari’a 6:4-6; Leviticus 19:18; Matta 22:36-40.

  Ta yaya ne Kiristoci suke nuna ƙaunarsu ga Allah da kuma maƙwabcinsu? (Mar. 6:34; A. M. 4:20; Rom. 15:2)