Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Labari na 34: Sabon Abinci

Labari na 34: Sabon Abinci

KA SAN abin da waɗannan mutanen suke tsinta daga ƙasa? Ya yi kama da ƙanƙara. Fari ne, ba shi da kauri kuma ƙwayoyi ne. Amma ba ƙanƙara ba ce, abinci ne.

Isra’ilawa suna tara manna

Bai wuce wata ɗaya ba da Isra’ilawa suka bar ƙasar Masar. Suna cikin daji. Kuma babu abinci sosai a nan, saboda haka mutanen suka fara mita, suna cewa: ‘Da ma Jehobah ya kashe mu a ƙasar Masar. Aƙalla, a can muna samun dukan irin abincin da muke so.’

Saboda haka, Jehobah ya ce: ‘Zan zuɓo da abinci daga sama.’ Haka kuwa Jehobah ya yi. Washegari da Isra’ilawan suka ga wannan farin abin da suka zubo, suka fara tambayar junansu: ‘Menene wannan?’

Musa ya ce: ‘Wannan shi ne abincin da Jehobah ya ba ku ku ci.’ Mutanen suka kira shi MANNA. Ɗanɗanonsa kamar na waina ne da aka yi da zuma.

‘Ku ɗebi iyakar abin da kowa zai iya ci,’ Musa ya gaya wa mutanen. A kowace safiya sai su je su ɗiba. Amma, idan rana ta fito ta yi zafi, manna da suka ƙyale a ƙasa sai ya narke.

Musa kuma ya ce musu: ‘Kada kowa ya ɗiba domin gobe.’ Amma wasu mutane ba su saurara ba. Ka san abin da ya faru? Washegari manna da suka ajiye sai ya cika da tsutsa, ya fara wari!

Amma da rana ɗaya a mako, da Jehobah ya gaya wa mutane su ɗebi manna domin abincinsu na kwana biyu. Wannan ita ce rana ta shida. Kuma Jehobah ya ce su ci su rage domin gobe, domin ba zai zuɓo da manna ba a rana ta bakwai. Sa’ad da suka ajiye manna domin rana ta bakwai, bai cika da tsutsa ba kuma ba ya wari! Wannan wani abin al’ajabi ne!

A dukan shekaru da Isra’ilawa suka yi a cikin daji Jehobah ya ciyar da su da manna

Fitowa 16:1-36; Litafin Lissafi 11:7-9; Joshua 5:10-12Tambayoyi

 • A wannan hoton menene mutanen suke ɗiba daga ƙasa, kuma menene sunansa?
 • Wane umurni ne Musa ya bai wa mutanen game da ɗiban manna?
 • Menene Jehobah ya gaya wa mutanen su yi a rana ta shida, kuma me ya sa?
 • Wane abin al’ajabi Jehobah yake yi sa’ad da aka adana abincin domin rana ta bakwai?
 • Jehobah ya ciyar da mutanen da manna na shekara nawa ne?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Fitowa 16:1-36 da kuma Litafin Lissafi 11:7-9.

  Menene Fitowa 16:8 ya nuna game da yadda ya kamata mu daraja waɗanda Allah ya naɗa a ikilisiyar Kiristoci? (Ibran. 13:17)

  A cikin daji, ta yaya aka tuna wa Isra’ilawa game da dogararsu ga Jehobah kowace rana? (Fit. 16:14-16, 35; K. Sha 8:2, 3)

  Wace ma’ana ce Yesu ya ba wa manna, kuma ta yaya muka amfana daga wannan “gurasa daga cikin sama”? (Yoh. 6:31-35, 40)

 • Ka karanta 5:10-12.

  Shekara nawa ne Isra’ilawa suka yi suna cin manna, kuma ta yaya ne wannan ya gwada su, kuma menene za mu koya daga wannan labarin? (Fit. 16:35; Lit. Lis. 11:4-6; 1 Kor. 10:10, 11)