Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 6

Wane Bege Ne Matattu Suke da Shi?

Wane Bege Ne Matattu Suke da Shi?

1. Wanne abin farin ciki ne zai faru da matattu?

Sa’ad da Yesu ya isa ƙauyen Bait’anya kusa da Urushalima, abokinsa Li’azaru ya yi kwana huɗu da mutuwa. Yesu ya tafi kabarin tare da Martha da Maryamu, ’yan’uwan mamacin. Ba da daɗewa ba, jama’a suka taru. Ka yi tunanin irin farin cikin da Martha da Maryamu suka yi sa’ad da Yesu ya ta da Li’azaru daga matattu!​—Karanta Yohanna 11:21-24, 38-44.

Martha ta ba da gaskiya cewa matattu za su tashi. Ta san cewa Jehobah zai ta da matattu kuma za su sake rayuwa a duniya.​—Karanta Ayuba 14:14, 15.

2. Mene ne yanayin matattu?

Allah ya gaya wa Adamu: “Turɓaya ne kai, ga turɓaya za ka koma.”​—FARAWA 3:19.

An halicci ’yan Adam daga turɓaya. (Farawa 2:7; 3:19) Ba abin da ke cikin jikinmu da ke rayuwa bayan mun mutu. Mu nama ne da jini, saboda haka babu kome da ke barin jikinmu sa’ad da muka mutu. Sa’ad da muka mutu, sai ƙwaƙwalwarmu ta daina aiki kuma shawarwarinmu su ƙare. Shi ya sa Li’azaru bai faɗi kome ba game da wani abin da ya faru da shi sa’ad da ya mutu, domin bai san kome ba.​—Karanta Zabura 146:4; Mai-Wa’azi 9:5, 6, 10.

Hakika, Allah ba ya azabtar da mutane da wuta sa’ad da suka mutu. Tun da Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa matattu ba su san kome ba, koyarwar wutar jahannama ƙarya ce da ke ɓata sunan Allah. Jehobah yana ƙyamar ra’ayin azabtar da mutane a cikin wuta.​—Karanta Irmiya 7:31.

Ka kalli bidiyon nan Wane Yanayi Ne Matattu Suke Ciki?

3. Matattu za su iya yi mana magana ne?

Matattu ba za su iya yin magana ba kuma ba za su iya jin magana ba. (Zabura 115:17) Amma, wasu mala’iku mugaye ne, suna iya yi wa mutane magana kuma su yi kamar matattu ne suke magana. (Yahuda 6) Jehobah ya haramta yin magana da matattu.​—Karanta Kubawar Shari’a 18:10, 11.

4. Su waye ne za a ta da daga matattu?

Za a ta da miliyoyin mutane da suka mutu don su sake rayuwa a duniya. Za a ta da wasu da suka aikata mugunta domin ba su san Jehobah ba.​—Karanta Zabura 37:29; Ayyukan Manzanni 24:15.

Waɗanda aka ta da daga matattu za su iya koyon gaskiya game da Allah kuma su ba da gaskiya ga Yesu ta wajen yi masa biyayya. (Ru’ya ta Yohanna 20:11-13) Waɗanda suka yi abubuwa masu kyau bayan an ta da su daga matattu za su rayu har abada a duniya.​—Karanta Yohanna 5:28, 29.

5. Mene ne tashin matattu ya koya mana game da Jehobah?

Tashin matattu ya yiwu ne saboda Jehobah ya aiko da Ɗansa ya ba da ransa domin mu. Saboda haka, tashin matattu ya koya mana cewa Jehobah Allah ne mai ƙauna da kuma alheri. Wane ne kake son ka gani sa’ad da aka ta da mutane daga matattu?​—Karanta Yohanna 3:16; Romawa 6:23.