Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 9

Me Zai Sa Iyalinka Ta Yi Farin Ciki?

Me Zai Sa Iyalinka Ta Yi Farin Ciki?

1. Me ya sa yin aure bisa doka yake da muhimmanci don iyali ta yi farin ciki?

Albishiri game da aure daga wurin Jehobah ne. Allah mai farin ciki ne kuma yana son iyalai su yi farin ciki. (1 Timotawus 1:11) Shi ne ya kafa aure. Auren da aka yi bisa doka yana sa iyaye da kuma yara farin ciki kuma su ƙaunaci juna.

Ya kamata Kiristocin da suke son su yi biyayya ga Allah su yi rajistar aurensu bisa dokar ƙasarsu. Jehobah yana son mata da miji su kasance da aminci ga juna. (Ibraniyawa 13:4) Ya tsani kashe aure. (Malakai 2:16) Jehobah ya yarda Kiristoci su kashe aure kuma su sake yin wani idan ɗaya daga cikinsu ya yi zina.​—Karanta Matta 19:3-6, 9.

2. Yaya ya kamata mata da miji su bi da juna?

Jehobah ya halicci maza da mata domin su taimaka wa juna a aure. (Farawa 2:18) A matsayin shugaban iyali, maigida ne ya kamata ya kasance kan gaba wajen biyan bukatun iyalinsa kuma ya koya musu game da Allah. Ya kamata ya nuna ƙauna da sadaukarwa ga matarsa. Ya kamata mata da miji su nuna ƙauna da daraja ga juna. Tun da dukan maza da mata ajizai ne, gafarta wa juna yana da muhimmanci sosai domin yana kawo farin ciki a aure.​—Karanta Afisawa 4:31, 32; 5:22-25, 33; 1 Bitrus 3:7.

3. Ya kamata ka rabu da matarka ne idan ba ka jin daɗin aurenku?

Idan kai da matarka kuna samun matsaloli, ku yi ƙoƙarin bi da juna cikin ƙauna. (1 Korintiyawa 13:4, 5) Kalmar Allah ba ta ce rabuwa ce za ta magance matsalolin da ake samu a aure ba.​—Karanta 1 Korintiyawa 7:10-13.

4. Yara, mene ne nufin Allah a gare ku?

Jehobah yana so ku kasance masu farin ciki. Yana ba ku shawara mafi kyau a kan yadda za ku ji daɗin ƙuruciyarku. Yana son ku amfana daga hikima da ƙwarewar iyayenku. (Kolosiyawa 3:20) Jehobah yana son ka more albarka da ke tattare da yi masa da kuma Ɗansa biyayya.​—Karanta Mai-Wa’azi 11:9–12:1; Matta 19:13-15; 21:15, 16.

5. Iyaye, mene ne yaranku suke bukata don su kasance masu farin ciki a rayuwa?

Ya kamata ku yi aiki tuƙuru don ku yi tanadin abinci da wurin kwana da kuma sutura ga yaranku. (1 Timotawus 5:8) Amma, don yaranku su kasance masu farin ciki, kuna bukatar ku koya musu su ƙaunaci Allah don su yi koyi da shi. (Afisawa 6:4) Misalin da kuka kafa wajen nuna ƙauna ga Allah zai iya yin tasiri sosai a zuciyar yaranku. Idan umurnin da kuka ba da ya fito ne daga Kalmar Allah, hakan zai iya daidaita tunanin ’ya’yanku sosai.​—Karanta Kubawar Shari’a 6:4-7; Misalai 22:6.

Yara za su amfana idan iyaye suna ƙarfafa da kuma yaba musu. Suna kuma bukatar gyara da horo. Irin tarbiyyar nan tana kāre su daga halin da zai iya jawo musu baƙin ciki. (Misalai 22:15) Duk da haka, kada horo ya kasance mai tsanani ko kuma da azaba.​—Karanta Kolosiyawa 3:21.

Shaidun Jehobah suna wallafa littattafai da dama da aka rubuta musamman don taimaka wa iyaye da kuma yara. An ɗauko batutuwan da ke cikin waɗannan littattafan daga Littafi Mai Tsarki.​—Karanta Zabura 19:7, 11.