Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 8

Me Ya Sa Allah Ya Ƙyale Mugunta da Wahala?

Me Ya Sa Allah Ya Ƙyale Mugunta da Wahala?

1. Ta yaya aka soma mugunta?

Allah ya ƙyale mutane su mulke kansu, kuma hakan ya nuna cewa ba za su iya magance matsalarsu ba

An soma mugunta ne a duniya sa’ad da Shaiɗan ya tabka ƙarya ta farko. Shaiɗan kamiltaccen mala’ika ne a lokacin da aka halicce shi, amma ‘bai tsaya a kan gaskiya ba.’ (Yohanna 8:44) Ya yi sha’awar ainihin bautar da ake yi wa Allah. Shaiɗan ya tabka wa mace ta farko wato, Hauwa’u ƙarya kuma ya rinjaye ta ta yi masa biyayya maimakon Allah. Adamu da Hauwa’u sun yi rashin biyayya ga Allah. Matakin da Adamu ya ɗauka ne ya jawo wahala da mutuwa.​—Karanta Farawa 3:1-6, 19.

Sa’ad da Shaiɗan ya gaya wa Hauwa’u ta yi rashin biyayya ga Allah, yana tawaye ne ga Sarautar Allah. Kamar Shaiɗan, yawancin mutane sun ƙi Allah a matsayin Sarkinsu. Shi ya sa, Shaiɗan ya zama “sarkin duniya.”​—Karanta Yohanna 14:30; 1 Yohanna 5:19.

2. Halittun Allah suna da aibi ne?

Dukan abubuwan da Allah ya halitta suna da kyau. Mutane da kuma mala’ikun da Allah ya halitta suna da kamiltacciyar damar cika umurnin Allah. (Kubawar Shari’a 32:4, 5) Allah ya halicce mu da ’yancin zaɓen yin nagarta ko mugunta. Wannan ’yancin ya ba mu zarafin nuna ƙaunarmu ga Allah.​—Karanta Yaƙub 1:13-15; 1 Yohanna 5:3.

3. Me ya sa Allah ya ƙyale wahala ta ci gaba har yanzu?

Jehobah ya ɗan ba da lokaci ga waɗanda suke tawaye da Sarautar Allah. Me ya sa? Domin ya nuna cewa mutane ba za su taɓa yin nasara ba idan ba Allah ba ne ya yi sarautarsu. (Mai-Wa’azi 7:29; 8:9) An gane gaskiyar al’amarin bayan shekaru 6,000 da ’yan Adam suka yi sarautar kansu. ’Yan Adam masu sarauta sun kasa kawar da yaƙi da aikata laifi da rashin gaskiya da cuta.​—Karanta Irmiya 10:23; Romawa 9:17.

Akasin haka, waɗanda suka amince da sarautar Allah suna amfana. (Ishaya 48:17, 18) Ba da daɗewa ba, Jehobah zai halaka dukan gwamnatocin ’yan Adam. Waɗanda suka zaɓi sarautar Allah ne kawai za su zauna a duniya.—Ishaya 11:9.​—Karanta Daniyel 2:44.

Ka kalli bidiyon nan Me Ya Sa Allah Ya Ƙyale Mutane Su Sha Wahala?

4. Wane zarafi ne muke da shi saboda haƙurin da Allah ya yi?

Shaiɗan ya yi da’awar cewa ’yan Adam ba za su yi biyayya ga Jehobah cikin aminci ba. Za ka so ka ƙaryata Shaiɗan? Hakan zai yiwu! Haƙurin da Allah ya yi yana ba mu zarafin nuna ko mulkin Allah muke so ko na ’yan Adam. Muna nuna zaɓin da muka yi ta yadda muke rayuwa.​—Karanta Ayuba 1:8-12; Misalai 27:11.

5. Ta yaya za mu zaɓi Allah a matsayin Sarki?

Abin da muka yi ya nuna ko muna son Allah ya Mulke mu

Muna zaɓan Allah a matsayin Sarki sa’ad da muka biɗi bauta ta gaskiya kuma muka rungume ta kamar yadda Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki ta ce. (Yohanna 4:23) Idan muka guji saka hannu a siyasa da yaƙi kamar yadda Yesu ya yi, hakan zai nuna cewa muna ƙin Shaiɗan a matsayin sarkinmu.​—Karanta Yohanna 17:14.

Shaiɗan yana amfani da ikonsa don ya ɗaukaka yin lalata da kuma ayyuka masu lahani. Idan mun guji irin waɗannan ayyukan, wasu daga cikin abokanmu da danginmu suna iya yi mana ba’a ko hamayya. (1 Bitrus 4:3, 4) Saboda haka, muna da zaɓi. Ya kamata mu yi tarayya da mutanen da suke ƙaunar Allah. Kuma mu bi dokokinsa masu kyau da suka nuna yana ƙaunarmu. Idan muka yi hakan, za mu ƙaryata Shaiɗan a zargin da ya yi cewa babu wanda zai yi abin da Allah ya ce idan aka matsa wa matumin.​—Karanta 1 Korintiyawa 6:9,10; 15:33.

Ƙaunar da Allah yake wa mutane ta nuna cewa ba da daɗewa ba zai kawo ƙarshen mugunta da wahala. Waɗanda suka nuna cewa sun amince da hakan za su more rayuwa a duniya har abada.​—Karanta Yohanna 3:16.