DARASI NA 11
Ta Yaya Ne Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki Suke Amfanar Mu?
1. Me ya sa muke bukatar ja-gora?
Ta yaya dokokin Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu kāre ranmu da kuma na mutane?—ZABURA 36:9.
Mahaliccinmu ya fi mu hikima. Yana ƙaunarmu kuma yana kula da mu. Kuma bai halicce mu don mu ja-goranci kanmu ba. (Irmiya 10:23) Kamar yadda ƙananan yara suke bukatar ja-gorar iyayensu, hakan ma muke bukatar ja-gorancin Allah. (Ishaya 48:17, 18) Ƙa’idojin Littafi Mai Tsarki suna mana ja-gora kuma hakan baiwa ce daga Allah.—Karanta 2 Timotawus 3:16.
Dukan dokokin Jehobah Allah suna da amfani a gare mu. Sun nuna mana hanyar yin rayuwa mafi kyau a yau da kuma yadda za mu iya more albarka na har abada a nan gaba.—Karanta Zabura 19:7, 11; Ru’ya ta Yohanna 4:11.
2. Ta yaya Kalmar Allah take mana ja-gora?
Wasu koyarwar Littafi Mai Tsarki sun nuna mana abin da Allah yake son mu yi. Wasu dokoki kuma sun shafi fannoni dabam-dabam na rayuwa. (Kubawar Shari’a 22:8) Wajibi ne mu yi amfani da sanin yakamata don mu san abin da Allah yake son mu yi. (Misalai 2:10-12) Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa rai baiwa ne daga Allah. Wannan dokar za ta iya mana ja-gora a wurin aiki da gida da kuma sa’ad da muke tafiya. Kuma idan mun tuna da hakan, ba za mu sa ranmu da na wasu cikin haɗari ba.—Karanta Ayyukan Manzanni 17:28.
3. Waɗanne dokoki biyu ne suke da muhimmanci sosai?
Yesu ya yi magana game da dokoki biyu da suke da muhimmanci sosai. Na farko ya bayyana dalilin da ya sa ’yan Adam suke da rai, wato, don su san Misalai 3:6) Waɗanda suke yin biyayya ga wannan dokokin suna zama aminan Allah, suna yin farin ciki na gaske kuma za su samu rai na har abada.—Karanta Matta 22:36-38.
Allah, su ƙaunace shi kuma su bauta masa da aminci. Ya kamata mu yi la’akari da wannan dokar a duk shawarar da muke son mu yanke. (Doka ta biyu za ta iya sa mu samu dangantaka mai kyau da mutane. (1 Korintiyawa 13:4-7) Bin wannan doka ta biyu tana nufin cewa za mu bi da mutane kamar yadda Allah yake bi da mu.—Karanta Matta 7:12; 22:39, 40.
4. Ta yaya dokokin Littafi Mai Tsarki suke amfanar mu?
Dokokin Littafi Mai Tsarki suna koya wa iyalai yadda za su kasance da haɗin kai kuma su yi ƙaunar juna. (Kolosiyawa 3:12-14) Kalmar Allah tana kuma kāre iyalai ta wajen koya musu wata doka mai muhimmanci. Allah yana son aure ya dawwama.—Karanta Farawa 2:24.
Idan mun bin koyarwar Littafi Mai Tsarki, za mu iya kāre dukiyarmu da motsin ranmu. Alal misali, shugabannin aiki sun fi son mutanen da suke bin dokokin Littafi Mai Tsarki na yin gaskiya da kuma aiki tuƙuru. (Misalai 10:4, 26; Ibraniyawa 13:18) Kalmar Allah ta kuma koya mana yadda za mu yi wadar zuci da abubuwan da suke da muhimmanci kuma mu daraja abotarmu da Allah fiye da dukiya.—Karanta Matta 6:24, 25, 33; 1 Timotawus 6:8-10.
Yin biyayya ga dokokin Allah zai kyautata rayuwarmu. (Misalai 14:30; 22:24, 25) Alal misali, dokar Allah game da yin maye tana kāre mu daga muguwar cuta da kuma haɗarurruka. (Misalai 23:20) Jehobah yana son mu sha giya daidai wa daida. (Zabura 104:15; 1 Korintiyawa 6:10) Dokokin Allah suna amfanar mu ta wajen koya mana yadda za mu yi hankali da abubuwan da muke yi da kuma tunanin da muke yi. (Zabura 119:97-100) Amma, Kiristoci na gaskiya ba sa yin biyayya ga dokokin Allah don su amfane kansu kaɗai. Suna yin haka don su daraja Jehobah.—Karanta Matta 5:14-16.