Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yadda Za Ka Amfana Daga Wannan Ƙasidar

Yadda Za Ka Amfana Daga Wannan Ƙasidar

Wannan ƙasidar za ta taimaka maka ka ji daɗin koyon abubuwa daga Kalmar Allah, wato, Littafi Mai Tsarki. Nassosin da ke ƙarshen kowane sakin layi suna nuna inda za ka samu amsoshin tambayoyin nan da aka rubuta ɓaro-ɓaro.

Yayin da kake karanta ayoyin Littafi Mai Tsarki, ka yi la’akari da yadda suka amsa waɗannan tambayoyin. Kowanne Mashaidin Jehobah zai yi farin cikin taimaka maka ka san ma’anar Nassosin.​—Karanta Luka 24:32, 45.

Abin lura: Shaidun Jehobah ne suka wallafa dukan littattafan da aka ambata a cikin wannan ƙasidar.