Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 3

Albishirin da ke Cikin Littafi Mai Tsarki Ainihi Daga Allah Ne?

Albishirin da ke Cikin Littafi Mai Tsarki Ainihi Daga Allah Ne?

1. Wane ne Mawallafin Littafi Mai Tsarki?

Albishiri cewa mutane za su yi rayuwa har abada yana cikin Littafi Mai Tsarki. (Zabura 37:29) Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da ƙananan littattafai guda 66. Allah ya yi amfani da maza 40 masu aminci don su rubuta waɗannan littattafan. Musa ne ya rubuta littattafai guda biyar na farko wajen shekara 3,500 da ta shige. Manzo Yohanna ne ya rubuta littafi na ƙarshe fiye da shekara 1,900 da ta shige. Ra’ayin wane ne marubutan Littafi Mai Tsarki suka rubuta? Allah ya yi amfani da ruhunsa mai tsarki don ya bayyana musu abin da za su rubuta. (2 Sama’ila 23:2) Marubutan sun rubuta abin da Allah ya ce, ba abin da ke zuciyarsu ba. Saboda haka, Allah ne Mawallafin Littafi Mai Tsarki.​—Karanta 2 Timotawus 3:16; 2 Bitrus 1:20, 21.

Ka kalli bidiyon nan Wane ne Mawallafin Littafi Mai Tsarki?

2. Ta yaya za mu tabbata cewa abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki gaskiya ne?

Mun san cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce domin ya bayyana abubuwan da za su faru a nan gaba dalla-dalla kuma babu kuskure. Ba mutumin da zai iya yin haka. (Joshua 23:14) Allah Maɗaukaki ne kawai zai iya bayyana abubuwan da za su faru a nan gaba daidai.​—Karanta Ishaya 42:9; 46:10.

Ya kamata littafin da Allah ya wallafa ya yi dabam da sauran littattafai. Kuma haka Littafi Mai Tsarki yake. An buga da kuma rarraba biliyoyin kofi na Littafi Mai Tsarki a darurruwan harsuna. Ko da yake an rubuta Littafi Mai Tsarki da daɗewa, amma abin da ke cikinsa ya jitu da kimiyya a yau. Kuma abubuwan da marubutansa arba’in suka rubuta sun jitu da juna. * Ƙari ga hakan, Littafi Mai Tsarki ya bayyana ƙaunar Allah a gare mu kuma yana iya sa mutane su kyautata rayuwarsu. Waɗannan abubuwan da muka tattauna sun sa miliyoyin mutane su gaskata cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce.​—Karanta 1 Tasalonikawa 2:13.

Ka kalli bidiyon nan Ta Yaya Muka San Cewa Abin da Ke Littafi Mai Tsarki Gaskiya Ne?

3. Mene ne ke cikin Littafi Mai Tsarki?

Jigo na musamman na Littafi Mai Tsarki shi ne albishiri cewa Allah yana da kyakkyawar manufa don ’yan Adam. Littafi Mai Tsarki ya bayyana yadda ’yan Adam suka rasa gatan kasancewa cikin aljanna a duniya da daɗewa da kuma yadda za a mai da duniya aljanna a nan gaba.​—Karanta Ru’ya ta Yohanna 21:4, 5.

Kalmar Allah tana ɗauke da dokoki da ƙa’idoji da kuma shawarwari. Ƙari ga hakan, Littafi Mai Tsarki ya faɗi yadda Allah yake bi da mutane. Kuma hakan ya sa mun san halayensa. Saboda haka, Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka ka san Allah. Ya bayyana yadda za ka iya zama amininsa.​—Karanta Zabura 19:7, 11; Yaƙub 2:23; 4:8.

4. Ta yaya za ka iya fahimtar Littafi Mai Tsarki?

Wannan ƙasidar za ta taimaka maka ka fahimci Littafi Mai Tsarki ta wajen bayyana Kalmar Allah yadda Yesu ya yi. Yesu ya ambata nassin Littafi Mai Tsarki ɗaya bayan ɗaya kuma ya bayyana ma’anar “littattafai.”​—Karanta Luka 24:27, 45.

Sanin albishiri daga Allah abu mai ban farin ciki ne. Amma, wasu mutane ba za su yi farin ciki ba cewa kana karanta Littafi Mai Tsarki. Kada ka yi sanyin gwiwa. Kana bukatar ka san Allah idan kana son ka ji daɗin rayuwa har abada.​—Karanta Yohanna 17:3.

 

^ sakin layi na 3 Ka duba ƙasidar nan Littafi Don Dukan Mutane.