Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 13

Wane Albishiri ne Ake da Shi Game da Addini?

Wane Albishiri ne Ake da Shi Game da Addini?

1. Dukan addinai suna da kyau ne?

Akwai mutane masu kirki a dukan addinai. Abu mai kyau ne cewa Allah ya ga waɗannan mutanen kuma yana kula da su. Amma abin baƙin ciki, mutane suna aikata mugunta da sunan addini. (2 Korintiyawa 4:3, 4; 11:13-15) Rahotanni daga kafofin yaɗa labarai suna nuna cewa waɗansu addinai suna saka hannu a ta’addanci da kisan ƙare-dangi da yaƙe-yaƙe da kuma ɓata ƙananan yara. Bayin Allah na gaskiya suna baƙin ciki sosai saboda waɗannan abubuwan!​—Karanta Matta 24:3-5, 11, 12.

Addini na gaskiya yana ɗaukaka Allah, amma addinin ƙarya yana ɓata wa Allah rai. Yana koyar da abubuwa da ba sa cikin Littafi Mai Tsarki, waɗannan sun haɗa da koyarwar ƙarya game da Allah da kuma matattu. Amma, Jehobah yana son mutane su san gaskiya game da shi.​—Karanta Ezekiyel 18:4; 1 Timotawus 2:3-5.

2. Wane albishiri ne ake da shi game da addini?

Abin farin ciki ne cewa Allah ya san da dukan addinan da mabiyansu suke da’awa cewa suna ƙaunarsa amma Shaiɗan ne ainihi suke ƙauna. (Yaƙub 4:4) Kalmar Allah ta kira dukan addinan ƙarya “Babila Babba.” Kuma, Babila sunan wani birni ne inda aka soma bauta ta ƙarya bayan Rigyawa ta zamanin Nuhu. Nan ba da daɗewa ba, Allah zai halaka dukan addinan ƙarya da ke yaudarar da kuma wahalar da mutane.​—Karanta Ru’ya ta Yohanna 17:1, 2, 5, 16, 17; 18:8.

Albishirin bai ƙare a nan ba. Jehobah bai manta da mutane masu kirki da har yanzu suna cikin addinan ƙarya na duniya ba. Yana sa waɗannan su kasance da haɗin kai ta wajen koya musu gaskiya.​—Karanta Mikah 4:2, 5.

3. Me ya kamata mutane masu zuciyar kirki su yi?

Addini na gaskiya yana sa mutane su kasance da haɗin kai

Jehobah yana kula da mutanen da suke son gaskiya da kuma nagarta. Ya aririce su su bar addinin ƙarya. Mutane da suke ƙaunar Allah suna a shirye su canja rayuwarsu don su faranta wa Allah rai.​—Karanta Ru’ya ta Yohanna 18:4.

Sa’ad da mutane masu kirki suka ji bishara a ƙarni na farko, sun karɓe ta da farin ciki. Sun koyi salon rayuwa mai kyau, mai ma’ana da kuma bege daga wajen Jehobah. Sun kafa mana misali mai kyau domin sun karɓi bishara kuma sun mai da yin nufin Jehobah kan gaba a rayuwarsu.​—Karanta 1 Tasalonikawa 1:8, 9; 2:13.

Jehobah yana marabtar waɗanda suka bar addinan ƙarya. Idan ka yi na’am da gayyatar Jehobah, za ka zama amininsa kuma za ka kasance cikin ƙaunataccen iyali na waɗanda suke bauta wa Jehobah, kuma za ka samu rai na har abada.​—Karanta Markus 10:29, 30; 2 Korintiyawa 6:17, 18.

4. Ta yaya Jehobah zai sa mutanen dukan ƙasashen duniya su kasance da farin ciki?

Sanin cewa za a halaka addinan ƙarya albishiri ne. Hakan zai ’yantar da mutane a dukan duniya daga zalunci. Bayan haka, addinin ƙarya ba zai sake yaudarar ko kuma ware mutane ba. Duk waɗanda suke raye a lokacin za su bauta wa Allah makaɗaici na gaskiya cikin haɗin kai.​—Karanta Ru’ya ta Yohanna 18:20, 21; 21:3, 4.