Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 SASHE NA 3

Yaya Rayuwa Take a Lambun Adnin?

Yaya Rayuwa Take a Lambun Adnin?

Jehobah ya ba Adamu da Hauwa’u abubuwa da yawa masu kyau. Farawa 1:28

Jehobah ya halicci mace ta farko, Hauwa’u, kuma ya miƙa ta ga Adamu don ta zama matarsa.—Farawa 2:21, 22.

Jehobah ya halicce su da kamiltaccen jiki da hankali; ba tare da wani aibi ba.

Lambun Adnin ne gidansu, kuma wuri ne kyakkyawa mai koguna da ’ya’yan itatuwa da dabbobi.

Jehobah ya yi magana da su; kuma ya koyar da su. Idan suka saurare shi, za su rayu har abada a cikin Aljanna a duniya.

 Allah ya ce kada su ci ɗaya daga cikin itatuwan. Farawa 2:16, 17

Jehobah ya nuna wa Adamu da Hauwa’u wani itace mai ’ya’ya a cikin lambun kuma ya gaya musu cewa idan suka ci ’ya’yansa, za su mutu.

Ɗaya daga cikin mala’ikun ya yi wa Allah tawaye. Wannan mugun mala’ikan shi ne Shaiɗan Iblis.

Shaiɗan ba ya son Adamu da Hauwa’u su yi biyayya ga Jehobah. Saboda haka, ya yi amfani da maciji ya gaya wa Hauwa’u cewa idan ta ci daga ’ya’yan itacen, ba za ta mutu ba, amma za ta zama kamar Allah. Hakika, wannan ƙarya ce.—Farawa 3:1-5.