Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwa

Gabatarwa

Allah yana kama da uba mai ƙauna. 1 Bitrus 5:6, 7

Allah ne Mahaliccinmu, kuma yana kula da mu. Kamar yadda uba mai hikima da ƙauna yake ba ’ya’yansa umurni, hakazalika, Allah yana koya wa mutane a ko’ina hanya mafi kyau ta yin rayuwa.

Jehobah yana bayyana gaskiya masu tamani da suke sa mu farin ciki da bege.

Idan ka saurari Allah, zai yi maka ja-gora, zai kāre ka, kuma zai taimake ka ka magance matsalolinka.

Ba shi ke nan ba, za ka rayu har abada!

 Allah ya gaya mana, ‘Ku zo gareni, ku ji, kuma za ku rayu.’ Ishaya 55:3