Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 SASHE NA 11

Jehobah Yana Saurarar Mu Kuwa?

Jehobah Yana Saurarar Mu Kuwa?

Allah yana jin addu’o’inmu. 1 Bitrus 3:12

Jehobah “Mai-jin addu’a” ne. (Zabura 65:2) Yana son mu yi masa magana daga zukatanmu.

Ka yi addu’a ga Jehobah ba ga wani dabam ba.

 Za mu iya yin addu’a game da abubuwa da yawa. 1 Yohanna 5:14

Ka yi addu’a cewa a yi nufin Allah a sama da duniya.

Ka yi addu’a cikin sunan Yesu, don ka nuna cewa kana ɗaukan abin da ya yi maka da tamani.

Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka yi abin da yake da kyau. Za ka kuma iya yin addu’a game da samun abinci, aiki, mafaka, tufafi, da lafiyar jiki.