Koma ka ga abin da ke ciki

Jehobah Allah Ne da Ya Cancanci Mu San Shi

Jehobah Allah Ne da Ya Cancanci Mu San Shi

Jehobah Allah Ne da Ya Cancanci Mu San Shi

AKWAI wani abin da ya kamata ka sani da ba ka sani ba kuma don haka ba ka amfana daga abin? Idan abu kadan ne ka sani game da Allah, to, an bar ka a baya. Me ya sa? Domin kamar yadda miliyoyin mutane suka gano, sanin Allahn da ke cikin Littafi Mai Tsarki yana sa mu amfana sosai a rayuwa. Da zarar ka san Allah, za ka soma amfana, kuma za ka amfana har abada.

Jehobah ko Yahweh, wanda shi ne Mawallafin Littafi Mai Tsarki yana so mu san shi. Marubucin Zabura ya ce: “Bari su san cewa kai kadai ne mai suna Yahweh, Mafi Daukaka a dukan duniya.” Jehobah ya san cewa za mu amfana idan muka san shi. Allah da kansa ya ce: ‘Ni ne Yahweh Allahnku, wanda yake koya muku domin amfanin kanku.’ Ta yaya muke amfana daga sanin Jehobah, Allah Mafi Daukaka?​—Zabura 83:18; Ishaya 48:17.

Daya daga cikin amfanin da muke samu shi ne, sanin yadda za mu magance matsalolinmu, kasancewa da kwanciyar hankali da kuma samun bege na yin rayuwa na har abada. Kari ga haka, sanin Jehobah zai sa mu canja ra’ayinmu game da wasu batutuwa masu muhimmanci da ke damun mutane a duniya a yau. Wadanne batutuwa ke nan?

Rayuwarka Tana da Ma’ana Kuwa?

Duk da ci gaban da aka samu a bangaren fasaha, mutane sun ci gaba da yin tambayoyi masu muhimmanci kamar: ‘Me ya sa aka halicce ni? Me zai faru da ni bayan na mutu? Mene ne manufar rayuwa?’ Idan mutum bai san amsoshin tambayoyin nan ba, rayuwarsa ba za ta kasance da ma’ana ba. Shin, mutane da yawa ne suka san da haka? A wajen shekara ta 1997, an yi wani bincike a Jamus. A binciken, rabin mutanen da aka tattauna da su sun ce a yawancin lokuta ko a wasu lokuta, suna ganin rayuwa ba ta da ma’ana. Watakila a yankinku ma haka mutane suke ji.

Idan mutum bai san ma’anar rayuwa ba, zai yi wuya ya kafa makasudan da za su amfane shi. Shi ya sa yawancin mutane suna kokarin tara abin duniya ko neman aikin da zai sa su shahara. Duk da haka, ba sa samun gamsuwa kuma ba sa farin ciki. Rashin ganin amfanin rayuwarsu ya sa wasu mutane bakin ciki sosai har sun gwammace su mutu. Abin da ya faru da wata kyakkyawar yarinya ke nan. Mujallar nan International Herald Tribune, ta yi magana game da yariyar kuma ta ce, yarinyar ta taso a cikin iyalin “masu kudi da kuma gata.” Duk da cewa ita ’yar gata ce, ta kadaita sosai kuma ta dauka cewa rayuwarta ba ta da amfani. Hakan ya sa ta kashe kanta. Kila, kai ma ka taba jin labarin mutanen da suka kashe kansu tsabar bakin ciki.

Ka taba jin mutane suna cewa kimiyya za ta iya taimaka mana mu san kome game da rayuwa? Wata mujallar da aka rubuta a Jamus ta ce: “Ko da yake kimiyya tana da bayanai game da abubuwa da dama, ba za ta iya koya mana yadda za mu kusaci Allah, ko abin da ya dace da wanda bai dace ba. Koyarwar juyin halitta da sauran koyarwar ’yan kimiyya, ba sa ta’azantar da mu balle su kwantar mana da hankali.” Kimiyya ta sa mun gane abubuwa da yawa game da rayuwa amma ba za ta iya bayyana mana abin da ya sa aka halicce mu, da abin da zai faru da mu bayan mun mutu ba. Idan muka dogara da kimiyya, ba za mu taba gane ma’anar rayuwa ba. Shi ya sa wata jaridar da aka rubuta a Jamus ta ce, “mutane da dama a yau suna bukata a yi musu ja-goranci.”

Wane ne zai iya ja-gorance mu, in ba Mahaliccinmu ba? Tun da shi ne ya halicce mu, ba shakka ya san abin da ya sa muke duniyar nan. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah ya halicce mu ne domin mu yi rayuwa a duniya kuma mu kula da ita. Jehobah yana so mu yi koyi da halayensa kamar su, adalci da hikima da kuma kauna. Da zarar mun san dalilin da ya sa Jehobah ya halicce mu, za mu gane abin da sa muke rayuwa a duniya.​—Farawa 1:​26-28.

Me Za Ka Iya Yi?

Idan a dā ka yi tambayoyin nan: ‘Me ya sa aka halicce ni? Me zai faru da ni bayan na mutu? Mene ne manufar rayuwa?’ Kuma ba ka samu amsoshinsu ba, Littafi Mai Tsarki ya ce idan ka kusaci Jehobah, za ka sami amsoshinsu. Yesu ya ce: “Rai na har abada kuwa shi ne, mutane su san ka, kai da kake Allah makadaici na gaskiya, su kuma san Yesu Almasihu wanda ka aiko.” Littafi Mai Tsarki ya kuma karfafa ka ka nuna kauna kuma ka kokarta don ka nuna cewa kana so ka rayu a karkashin Mulkin Allah. Hakan zai sa rayuwarka ta kasance da ma’ana kuma za ka sami begen jin dadin rayuwa a nan gaba. Za ka sami duka amsoshin tambayoyin da kake da su game da rayuwa.​—Yohanna 17:3; Mai-Wa’azi 12:13.

Ta yaya za ka amfana? Bari mu ga yadda wani mutum mai suna Hans ya amfana. * A dā, Hans ya yarda cewa akwai Allah, amma bai dauke shi da muhimmanci ba. A lokacin, Hans yana shan kwayoyi, yana lalata da mata, yana aikata laifi kuma yana son gudu a kan manyan babura. Hans ya ce: “Amma hakan bai sa ni farin ciki ba.” Da yake wajen shekara 25, ya tsai da shawarar koya game da Allah ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki. Da Hans ya dada sanin Jehobah da manufar rayuwa, sai ya canja halinsa kuma ya yi baftisma ya zama Mashaidin Jehobah. Yanzu, ya yi shekara goma yana hidima ta cikakken lokaci. Ya ce: “Bautar Jehobah ita ce hanyar rayuwa mafi inganci. Ba abin da ya kai hakan. Sanin Jehobah ya taimaka min in san manufar rayuwa.”

Ba dalilin da ya sa Allah ya halicce mu ne kadai batun da ke damun mutane ba. Yayin da abubuwa suke dada muni a duniya, akwai wata tambayar da mutane da dama suke yi.

Me Ya Sa Munanan Abubuwa Suke Faruwa?

Idan wani bala’i ya auku, wadanda abin ya shafa sukan yi tambaya su ce: Me ya sa hakan ya faru? Idan ka san abin da ya sa wani abu ya faru, hakan zai taimaka maka ka iya jimrewa kuma ba za ka yi fushi ba. Bari mu ga labarin wata mai suna Bruni da ya tabbatar da gaskiyar maganar nan.

Bruni ta ce: “A shekarun baya, ’yata ta rasu. Na yi imani cewa akwai Allah, kuma hakan ya sa na je wurin wani fasto don ya ta’azantar da ni. Amma da na gaya masa abin da ke damuna, sai ya ce Allah ne ya dauki ’yata Susanne ya kai ta sama. Yanzu ta dawo mala’ika. Abin da ya gaya min ya jijjiga ni sosai kuma hakan ya sa na tsane Allah.” Bruni ta yi shekaru da yawa tana fama da bakin ciki. Ta kuma ce: “Sai wata rana wata Mashaidiyar Jehobah ta nuna min daga Littafi Mai Tsarki abin da ya sa bai kamata in tsane Allah ba. Ta gaya min cewa ba Jehobah ba ne ya dauki ’yata Susanne zuwa sama kuma ita ba mala’ika ba ce yanzu. Muna rashin lafiya ne don mu ajizai ne. Yanzu Susanne tana cikin kabari tana jiran lokacin da Jehobah zai ta da ita daga mutuwa. Ta kuma koya min cewa ’yan Adam za su rayu har abada a cikin aljanna a duniya nan ba da dadewa ba. Da na soma gane halayen Jehobah, hakan ya sa na kusace shi kuma na sami sauki a zuciyata.”​—Zabura 37:29; Ayyukan Manzanni 24:15; Romawa 5:12.

Miliyoyin mutane sukan shan wahala idan suka tsinci kansu cikin wata masifa, ko ana yaki, ko matsananciyar yunwa, ko kuma bala’i ya auku a inda suke. Da Bruni ta gani a cikin Littafi Mai Tsarki cewa ba Jehobah ne yake sa munanan abubuwa suke faruwa ba, bai so mutane su sha wahala ba, kuma nan ba da dadewa ba zai cire shan wahala, hakan ya kwantar mata da hankali. Yadda munanan abubuwa suke dada karuwa a duniya, ya nuna cewa muna “kwanakin karshe.” Dukan mu muna so mu ga an daina shan wahala kuma abin da zai faru nan ba da dadewa ba ke nan.​—2 Timoti 3:​1-5; Matiyu 24:​7, 8.

Ta Yaya Za Mu San Allah?

A dā, Hans da Bruni ba su fahimci halayen Allah sosai ba. Sun yarda cewa akwai Allah amma ba su san abubuwa da yawa game da shi ba. Da suka yi kokari sosai don su dada sanin Jehobah kuma su kusace shi, sun sami amsoshin tambayoyinsu kuma hakan ya gamshe su. Hakan ya sa hankalinsu ya kwanta kuma sun kasance da bege. Abin da ya faru da miliyoyin Shaidun Jehobah ke nan.

Kafin mutum ya san Jehobah, wajibi ne ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki don a wurin ne zai koya game da Jehobah kuma ya san abin da yake so ya yi. Wasu mutane da suka yi rayuwa wajen shekaru 2,000 da suka shige ma sun yi hakan. Luka ya rubuta cewa wadanda suke ikilisiyar Biriya, “sun karbi maganar hannu biyu-biyu [daga Bulus da Sila]. Suna ta binciken rubutacciyar maganar Allah kullum, su gani ko abin da Bulus ya fada gaskiya ne.”​—Ayyukan Manzanni 17:​10, 11.

A karni na farko, Kiristoci sukan hadu don su yi taron ibada tare. (Ayyukan Manzanni 2:​41, 42, 46; 1 Korintiyawa 1:​1, 2; Galatiyawa 1:​1, 2; 2 Tasalonikawa 1:1) Haka ma a yau. Shaidun Jehobah sukan yi taro don su koya wa mutane yadda za su kusaci Jehobah kuma su san yadda za su bauta masa da farin ciki. Ga wani amfani kuma da za ka samu idan kana tarayya da Shaidun Jehobah. Shaidun Jehobah suna koyi da halayen Jehobah. Don haka idan kana zuwa taronsu, za su taimaka maka ka dada sanin Jehobah kuma ka yi koyi da shi.​—Ibraniyawa 10:​24, 25.

Zai dace ka yi ta irin wannan kokarin don kawai ka san Allah? Ba shakka, sai ka kokarta. Idan muna so mu cim ma burinmu a kan wasu abubuwa a rayuwa, ai dole mu yi kokari sosai, ko ba haka ba? Ga labarin wani mai tsere da yake kokari sosai kafin lokacin wasa. Wani mai tsere da ya sami lambar yabo na zinariya sau uku mai suna Jean-Claude Killy, ya bayyana abin da mutum zai yi kafin ya sami nasara a manyan wasannin duniya. Ya ce: “Za ka soma shiri shekara 10 kafin wasan, kuma ka yi shekaru kana ta tunani a kan wasan kowace rana . . . Aiki ne da za ka yi kowace rana a cikin shekara. Za ka bukaci ka rika motsa jikinka kullum kuma ka rika tunani a kan abin da kake yi.” Duk wannan kokarin ana yin sa ne don tseren da mai yiwuwa zai dauki minti goma kawai! Don haka, za mu amfana sosai idan muka kokarta mu san Jehobah.

Dangantakar da Za A Iya Dada Karfafa Ta

Babu wanda ba ya so ya san manufar rayuwa. Don haka, idan kana ganin rayuwarka ba ta da ma’ana ko ba ka san abin da ya sa munanan abubuwa suke faruwa ba, ka yi kokari ka san Jehobah. Koya game da shi zai kyautata rayuwarka a yanzu da kuma har abada.

Shin, za mu san kome game da Jehobah ne a nan gaba? Ko bayinsa da suka yi shekaru da yawa suna bauta masa ma suna koyan sabbin abubuwa game da shi har yanzu. Sanin abubuwan nan suna sa mu farin ciki kuma za su sa mu dada kusantar sa. Ba shakka, za ka yarda da abin da manzo Bulus ya rubuta cewa: “Ina misalin zurfin yawan hikimar Allah! Zurfin saninsa kuma marar iyaka ne! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban bincike, hanyoyin al’amuransa sun wuce gaban ganewa! ‘Wa ya taba sanin zuciyar Ubangiji? Wa ya taba zama abokin shawararsa?’”​—Romawa 11:​33, 34.

[Ƙarin bayani]

^ sakin layi na 12 An canja sunayen.

[Akwati]

Mutane sun ci gaba da yin tambayoyi masu muhimmanci kamar: ‘Me ya sa aka halicce ni? Me zai faru da ni bayan na mutu? Mene ne manufar rayuwa?’

[Akwati]

“Da na soma gane halayen Jehobah, hakan ya sa na kusace shi”

[Akwati]

“Bautar Jehobah ita ce hanyar rayuwa mafi inganci. Ba abin da ya kai hakan. Sanin Jehobah ya taimaka min in san manufar rayuwa”