Me ya sa Ya Kamata Mu Yi Addu’a Cikin Sunan Yesu?

Me ya sa Ya Kamata Mu Yi Addu’a Cikin Sunan Yesu?

YESU ya koyar da mutane game da addu’a sau da yawa. A lokacin da yake duniya, malaman addinai sukan yi addu’a a “kan hanya.” Me ya sa? “Domin mutane su gan su.” Babu shakka, suna yin haka ne don a ce su masu ibada ne sosai. Da yawa daga cikin su sukan yi doguwar addu’a kuma su ta maimaita abu daya. Suna ganin kamar “dogon surutu ne” zai sa Allah ya ji su. (Matiyu 6:​5-8) Yesu ya nuna cewa hakan bai da amfani, kuma ya taimaka wa mutanen kirki su san abubuwan da za su guje wa sa’ad da suke addu’a. Ban da haka, Yesu ya koya musu wasu abubuwa game da addu’a.

Yesu ya koyar da cewa ya kamata addu’armu ta nuna cewa muna so a tsarkake sunan Allah, Mulkinsa ya zo, kuma a yi nufinsa a duniya. Ya kuma nuna cewa ya dace mu roki Allah ya biya bukatunmu. (Matiyu 6:​9-13; Luka 11:​2-4) Yesu ya yi amfani da misalai don ya nuna mana cewa muna bukatar mu nace, mu ba da gaskiya kuma mu kasance da tawali’u idan muna so Allah ya ji addu’armu. (Luka 11:​5-13; 18:​1-14) Amma ba koyarwa kawai Yesu ya yi ba, ya nuna hakan a rayuwarsa.​—Matiyu 14:23; Markus 1:35.

Babu shakka, abin da Yesu ya koya wa almajiransa ya taimaka musu su inganta addu’o’insu. Amma Yesu ya jira sai darensa na karshe a duniya kafin ya koya musu darasi mafi muhimmanci game da addu’a.

“Sabon Tsarin Yin Addu’a”

A darensa na karshe a duniya, Yesu ya dauki lokaci sosai yana karfafa manzanninsa masu aminci. Kuma a lokacin ne ya koya musu wani sabon abu. Yesu ya ce: “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina.” Bayan haka, ya karfafa su da cewa: “Duk dai abin da kuka roka cikin sunana zan yi, domin Uban ya sami daukaka ta wurin Dan. Ko mene ne kuka roka a cikin sunana, zan yi shi.” Da yake kammala maganarsa, sai ya ce: “Har yanzu dai, ba ku roki ko wani abu a cikin sunana ba. Ku roka, za ku samu, domin farin cikinku ya zama cikakke.”​—Yohanna 14:​6, 13, 14; 16:24.

Wadannan kalmomin suna da muhimmanci sosai. Wani littafin bincike ya ce a lokacin ne aka sami “sabon tsarin yin addu’a.” Yesu ba ya nufin cewa a rika yin addu’a gare shi maimakon Allah. Amma yana nuna mana sabon hanyar da za mu yi addu’a ga Jehobah ne.

Allah ya saba sauraron addu’ar bayinsa masu aminci tun zamanin dā. (1 Sama’ila 1:​9-19; Zabura 65:2) Amma tun daga lokacin da Allah ya yi yarjejeniya da al’ummar Isra’ila, ya zama wajibi duk wanda yake so a ji addu’arsa ya yarda cewa Isra’ila ce al’ummar da Allah ya zaba. Kuma daga lokacin da Sulemanu ya gina haikali, ya zama wajibi kowa ya yarda cewa haikalin ne inda Allah ya zaba a rika masa hadaya. (Maimaitawar Shari’a 9:29; 2 Tarihi 6:​32, 33) Amma wannan tsarin ba abin da zai kasance har abada ba ne. Kamar yadda manzo Bulus ya rubuta, Dokar da aka bayar ta hannun Musa da hadayun da aka yi a haikali ‘kwatanci ne kawai na abubuwa masu kyau wadanda suke a gaba, ba su ne ainihin abubuwan nan ba.’ (Ibraniyawa 10:​1, 2) Dole a kawar da kwatancin don ainihin abin ya kasance. (Kolosiyawa 2:17) Tun shekara ta 33 bayan haihuwar Yesu, Allah ya daina bukatar bayinsa su bi Dokar Musa don su sami amincewarsa. A maimakon haka, samun amincewar Allah ya dangana ne ga yin biyayya ga Yesu Kristi, wanda Dokar ta ce mu bi.​—Yohanna 15:​14-16; Galatiyawa 3:​24, 25.

Sunan “da Ya Fi Kowane Suna”

Yesu ya nuna mana hanya mafi inganci na yin magana da Jehobah. Ya nuna mana cewa shi kamar aboki ne mai iko a gare mu, kuma ta wurin sa ne Allah yake jin addu’o’inmu. Me yake taimaka wa Yesu ya yi hakan a madadin mu?

Tun da an haife mu cikin zunubi, ba abin da za mu iya yi ko kuma hadayun da za mu iya bayarwa da za su wanke mu daga zunubin nan ko su sa mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah, Allah mai tsarki. (Romawa 3:​20, 24; Ibraniyawa 1:​3, 4) Amma Yesu ya ba da ransa marar aibi don ya ceto ’yan Adam da suka ba da gaskiya. (Romawa 5:​12, 18, 19) Yanzu haka, Jehobah zai iya gafarta zunuban wadanda suka roke shi kuma za su iya kasancewa da ‘karfin halin’ yin addu’a a sake. Amma sai sun yi imani da hadayar Yesu kuma sun yi addu’a cikin sunansa kafin hakan ya yiwu.​—Afisawa 3:​11, 12.

Yin addu’a a cikin sunan Yesu zai nuna cewa mun yi imani da matsayinsa na yin nufin Allah a hanyoyi uku: (1) Shi ne “Dan Rago na Allah” wanda hadayarsa ta bude mana hanyar samun gafara daga zunubanmu. (2) Jehobah ya ta da shi daga mutuwa kuma yanzu shi “babban firist” ne da yake taimaka mana mu amfana daga hadayarsa. (3) Shi ne “hanya,” wato ta wurin sa ne kadai za mu iya yin addu’a ga Jehobah.​—Yohanna 1:29; 14:6; Ibraniyawa 4:​14, 15.

Yin addu’a a cikin sunan Yesu yana girmama Yesu. Ya dace mu girmama Yesu a wannan hanyar domin nufin Jehobah ne “ga sunan nan Yesu kowace gwiwa za ta durkusa, . . . kowane harshe kuma ya shaida cewa Yesu Almasihu Ubangiji ne, domin a daukaka Allah Uba.” (Filibiyawa 2:​10, 11) Mafi muhimmanci ma, yin addu’a a cikin sunan Yesu yana daukaka Jehobah, wanda ya ba da hadayar Dansa don amfaninmu.​—Yohanna 3:16.

Mu yi addu’a ‘da dukan zuciyarmu,’ ba kawai mu yi ta maimaita kalmomi ba

Littafi Mai Tsarki ya kira Yesu da lakabi da kuma sunaye dabam-dabam don ya nuna mana irin matsayin da Yesu yake da shi. Kuma sun taimaka mana mu fahimci albarkun da muke samu don abin Yesu ya yi a baya, da abin yake yi yanzu, da kuma abin da zai yi a nan gaba. (Ka duba akwatin nan, “ Matsayin Yesu”.) Hakika, Allah ya ba wa Yesu ‘sunan da ya fi kowane suna.’ * An ba shi dukan iko a sama da kuma duniya.​—Filibiyawa 2:9; Matiyu 28:18.

Bai Kamata Ya Zama Abin da Muka Haddace Kawai Ba

Wajibi ne mu yi addu’a a cikin sunan Yesu idan muna so Jehobah ya ji addu’armu. (Yohanna 14:​13, 14) Amma kada mu rika ce, “a cikin sunan Yesu” don kawai mun saba fadan haka. Me ya sa?

Ga wani misali. Idan wani dan kasuwa ya tura maka wasika, kila a karshen wasikar za ka gani, “ni ne naka.” Kana ganin dan kasawar ya rubuta hakan don yana kaunar ka ne ko yana bin ka’idar rubuta wasiku ne kawai? Bai kamata yin amfani da sunan Yesu ya zama haka ba. Ko da yake Littafi Mai Tsarki ya umurce mu mu “yi ta yin addu’a babu fasawa,” mu yi hakan ‘da dukan zuciyarmu,’ ba kawai mu yi ta maimaita kalmomi ba.​—1 Tasalonikawa 5:17; Zabura 119:145.

Ta yaya za ka guji yin amfani da furucin nan “a cikin sunan Yesu” kamar ka’idar da ya kamata ka rika bi kawai? Ka yi tunani mai zurfi game da kyawawan halayen Yesu. Ka kuma yi tunani game da abubuwan da ya riga ya yi maka da kuma wadanda zai yi maka a gaba. Sa’ad da kake addu’a, ka gode wa Jehobah kuma ka yaba masa don yadda ya yi amfani da Dansa. Yin haka zai sa ka ba da gaskiya ga alkawarin da Yesu ya yi cewa: “Uba zai ba ku duk abin da kuka roka a cikin sunana.”​—Yohanna 16:23.

^ sakin layi na 14 Bisa ga kamus mai suna, Expository Dictionary of New Testament Words, da Vine ya rubuta, kalmar Helenanci da aka fassara “suna” tana nufin “abin da sunan yake bayyana game da mai shi, da matsayinsa da ikonsa da halinsa [da kuma] daukakarsa.”