Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Yadda Za A Bi Bayanin da Ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi

Yadda Za A Bi Bayanin da Ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi

Tun daga watan Janairu 2018, an soma nuna yadda za mu yi wa’azi a shafin farko na Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu. Ta yaya za mu bi bayanin da aka bayar?

Sa’ad da Aka Ba Mu Aiki A Taro: Ka yi amfani da tambaya da nassi da kuma tambaya don ziyara ta gaba da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Amma hakan ba ya nufin cewa za ka bi abin da ke bidiyon kalma bayan kalma. Kana iya amfani da yanayi dabam da gabatarwa dabam. Ban da haka ma, za ka iya yin bayani a wata hanya dabam da dai sauran su. Kana ma iya ba da ɗaya daga cikin littattafanmu na nazari ko da ba a umurce ka ka yi hakan ba.

Sa’ad da Kake Wa’azi: Bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi suna taimaka mana ne mu san hanyoyin tattaunawa da mutane. Idan mutumin ya ji daɗin wa’azin kuma yana so ku ci gaba da tattaunawar, kana iya amfani da bayanin da ke komawa ziyara don ka yi hakan. Kana iya canja yadda za ka gabatar da bayanin ko kuma ka yi amfani da wani abu dabam. Shin batun da aka tattauna makon da ya shige ko kuma wani nassi dabam ne zai fi jawo hankalin mutane a yankinku? Shin mutane a yankinku sun fi jin daɗin tattauna wani abu da ya faru a yankin ko kuma labarai na kwana kwanan nan? Za ka iya yin amfani da bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi a hanyoyi dabam-dabam, amma niyyarka ita ce ka yi kome “saboda labari mai daɗi” don ka iya gaya wa mutane.​—1Ko 9:​22, 23.