Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Mene ne Ra’ayin Jehobah?

Mene ne Ra’ayin Jehobah?

Kafin mu yanke kowace irin shawara, ya kamata mu tambayi kanmu, ‘Mene ne ra’ayin Jehobah game da hakan?’ Ko da yake ba za mu iya sanin ra’ayin Jehobah game da kome ba, ya bayyana mana a cikin Kalmarsa abubuwan da za su taimaka mana mu yi “kowane irin kyakkyawan aiki.” (2Ti 3:​16, 17; Ro 11:​33, 34) Yesu ya san abin da Jehobah yake so kuma ya mai da hankali ga hakan. (Yoh 4:34) Bari mu bi misalin Yesu kuma mu yi iya ƙoƙarinmu wajen aikata abubuwan da za su faranta ran Jehobah.​—Yoh 8:​28, 29; Afi 5:​15-17.

KU KALLI BIDIYON NAN KU RIƘA TUNANI A KAN ABIN DA JEHOBAH YAKE SO (L.FI 19:18), SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Me ya sa ya kamata mu riƙa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki?

  • Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne ya kamata mu tuna sa’ad da muke zaɓan waƙoƙin da za mu ji?

  • Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne ya kamata mu tuna sa’ad da muke zaɓan tufafin da za mu saka?

  • A waɗanne fannonin rayuwa ne kuma ya kamata mu yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki?

  • Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da sanin abin da Jehobah yake so?

Mene ne shawarwarina suke nunawa game da dangantakata da Jehobah?