Wata ta natsu sosai sa’ad da take nazari da kuma bimbini

LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU Yuni 2017

Gabatarwa

Yadda za a iya ba da mujallar Awake! da kuma koyar da gaskiya game da rai da Allah ya ba mu kyauta. Ka yi amfani da misalan nan don ka rubuta taka gabatarwar.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Maganar Jehobah Tana Cika a Koyaushe

Annabcin da Irmiya ya yi cewa za a halaka Babila kuma ba za a sake zama a cikinta ba ya cika.

RAYUWAR KIRISTA

Ka Gaskata da Alkawuran Jehobah Kuwa?

Joshua ya ga cewa babu ko daya cikin alkawuran da Jehobah ya yi wa Isra’ilawa da bai cika ba. Me zai taimaka mana mu dogara ga alkawuran Jehobah sosai?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Zama Masu Hakuri Zai Taimaka Mana Mu Jimre

Mene ne ya taimaka wa Irmiya ya jimre duk da wahalar da yake sha? Ta yaya za mu yi shiri don kalubalen da za mu fuskanta a nan gaba?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Ezekiyel Ya Yi Shelar Sakon Allah da Farin Ciki

Jehobah ya ba Ezekiyel littafi a cikin wahayi kuma ya ce ya ci littafin. Mene ne hakan yake nufi?

RAYUWAR KIRISTA

Ka Ji Dadin Yin Wa’azin Bishara

Yin wa’azi yana iya kasance mana da wuya a wasu lokuta, amma Allah yana so mu rika farin ciki yayin da muke bauta masa. Me za taimaka mana mu rika wa’azi da farin ciki?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Za a Saka Maka Alamar Samun Ceto Kuwa?

Wahayin Ezekiyel ya fara cika sa’ad da aka halaka Urushalima. Ta yaya yadda yake cika a zamaninmu yake shafanmu?

RAYUWAR KIRISTA

Ka Daraja Ka’idodin Jehobah Na Dabi’a

Wajibi ne mu daraja ka’idodin da Jehobah ya tsara game da dabi’a. Me ya sa? Kuma me ya sa yin hakan yake da muhimmanci sosai?