Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FITOWA 6-7

“Yanzu Za Ka Ga Abin da Zan Yi da Fir’auna”

“Yanzu Za Ka Ga Abin da Zan Yi da Fir’auna”

6:1, 6, 7; 7:4, 5

Kafin Jehobah ya kawo annoba a Masar kuma ya ceto Isra’ilawa daga bauta, ya gaya ma Isra’ilawan abin da zai yi. Za su ga ikon Jehobah a hanyar da ba su taɓa gani ba, kuma Masarawan za su san ko wane ne Jehobah. Sa’ad da alkawarin da Jehobah ya yi ya cika, hakan ya ƙarfafa bangaskiyar Isra’ilawan kuma ya sa su yi watsi da bautar ƙarya da suka koya a Masar.

Ta yaya labarin nan ya ƙarfafa bangaskiyarka cewa alkawuran Allah game da nan gaba za su cika?