Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FITOWA 10-11

Musa da Haruna Sun Nuna Karfin Zuciya

Musa da Haruna Sun Nuna Karfin Zuciya

10:3-6, 24-26, 28; 11:4-8

Musa da Haruna sun nuna ƙarfin zuciya sosai sa’ad da suke magana da Fir’auna wanda a lokacin shi ne sarki mafi iko a duk duniya. Me ya taimaka musu su yi hakan? Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da Musa, ya ce: “Ta wurin bangaskiya ne ya bar ƙasar Masar, ba tare da jin tsoron fushin sarki ba. Ya jimre saboda yana ganin wanda ido ba ya iya gani.” (Ibraniyawa 11:27) Musa da Haruna sun ba da gaskiya ga Allah sosai kuma sun dogara gare shi.

A wane irin yanayi ne za ka bukaci ƙarfin zuciya don ka yi wa’azi ga wani mai iko?