Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Saukaka Rayuwarmu Zai Sa Mu Yabi Allah

Saukaka Rayuwarmu Zai Sa Mu Yabi Allah

Akwai abubuwa da yawa da za su iya ɗauke hankalinmu a yau. Muna bukatar lokaci da kuzari sosai don yin saye-saye da biyan bashi da yin amfani da mallakarmu da kuma kula da su. Sa’ad da Yesu yake duniya, bai tattara kaya da yawa da za su janye hankalinsa daga yin wa’azi da ƙwazo ba.—Mt 8:20.

Ta yaya za ka iya sauƙaƙa rayuwarka don ka sami damar yin wa’azi da ƙwazo? Za ku iya yin canje-canjen a iyalinku don wani cikinku ya soma hidimar majagaba? Ko da kana hidimar majagaba, kana barin kayan duniya su janye hankalinka daga hidimar? Za mu yi farin ciki sosai kuma mu yi rayuwa mafi inganci idan muka sauƙaƙa rayuwarmu.—1Ti 6:7-9.

Hanyoyin da zan iya sauƙaƙa rayuwata.