Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Za Ka Iya Hidimar ta Shekara Daya?

Za Ka Iya Hidimar ta Shekara Daya?

Wace hidima ke nan? Hidimar majagaba na kullum! Idan ka yi wannan hidimar, za ka yi farin ciki sosai kuma ka sami albarka!—Mis 10:22.

IDAN KANA HIDIMAR, ZA KA . . .

  • ƙware kuma ka ji daɗin wa’azi

  • ƙarfafa dangantakarka da Jehobah. Kuma yayin da kake gaya wa wasu game da shi, za ka riƙa tunasar da kanka halayensa masu kyau

  • yi farin ciki da wadar zuci domin ka san cewa kana biɗan Mulkin Allah farko kuma kana ba da kai don taimaka ma wasu.—Mt 6:33; A. M. 20:35

  • sami damar halartan taron da ake yi da majagaba a lokacin ziyarar mai kula da da’ira da lokacin taron da’ira da kuma Makarantar Hidima ta Majagaba

  • sami damar gudanar da nazari da mutane da yawa

  • ji daɗin kasancewa da ’yan’uwa da dama a wa’azi kuma ku ƙarfafa juna.—Ro 1:11, 12