Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwa

Gabatarwa

HASUMIYAR TSARO

Tambaya: Da yake mutane sun kasa halaka Littafi Mai Tsarki, hakan ya nuna cewa littafin Allah ne, ko ba haka ba?

Nassi: Ish 40:8

Abin da Za Ka Ce: Waɗannan jerin talifofin sun tattauna yadda mutane suka kasa halaka Littafi Mai Tsarki.

HASUMIYAR TSARO (bangon baya)

Tambaya: Zan so in ji ra’ayinka game da wannan tambayar. [Ka karanta tambaya ta farko da ke shafi na 16.] Wasu suna ganin cewa addini abu ne da ’yan Adam suka tsara. Wasu kuma suna gani kamar Allah yana amfani da addini don ya sa mu kusace shi. Mene ne ra’ayinka?

Nassi: Yaƙ 1:27

Abin da Za Ka Ce: Wannan talifin ya ba da ƙarin bayani a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da wannan batun. Zan so in dawo don mu tattauna wasu abubuwa daga talifin.

ALBISHIRI DAGA ALLAH!

Tambaya: Wasu suna gani cewa karanta annabcin Littafi Mai Tsarki yana nan kamar karanta jaridu. Amma waɗanne cikin waɗannan annabcin ne ka ga suna cika?

Nassi: 2Ti 3:1-5

Abin da Za Ka Ce: Wannan ƙasidar ta nuna yadda waɗannan abubuwa suke da muhimmanci ga bayin Allah. [Ka tattauna darasi na 1, tambaya ta 2.]

KA RUBUTA TAKA GABATARWA

Ku yi amfani da fasalin da ke baya don rubuta taku gabatarwar wa’azi.