Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Ka Guji Yada Karya

Ka Guji Yada Karya

A yau, za a iya tura wa miliyoyin mutane saƙo da wuri ta rediyo da talabijin da intane ko kuma ta wasu hanyoyi. Amma bai kamata mutanen da suke bauta ma “Allah na gaskiya” su riƙa yaɗa ƙarya ko ba da gangan ba. (Za 31:​5, Littafi Mai Tsarki; Fit 23:1) Idan muka yaɗa ƙarya, za mu iya ɓata sunayen mutane. Idan kana so ka san ko wani abin da ka ji gaskiya ne, ka tambayi kanka:

  • ‘Na tabbata da wanda ya faɗi abin?’ Wataƙila wanda ya ba da labarin bai san ainihin gaskiyar batun ba. Mutane suna yawan ƙara gishiri a labari, don haka ka yi hankali wajen yaɗa labarin da ba ka san tushensa ba. Da yake an yarda da dattawan ikilisiya cewa suna faɗan gaskiya, zai dace su yi hankali wajen yaɗa labarai musamman waɗanda ba su san tushensu ba

  • ‘Maganar gulma ce?’ Idan labarin zai ɓata sunan mutum ko wani rukuni, zai dace kada mu yaɗa shi.​—K. Ma 18:8; Fib 4:8

  • ‘Za a iya gaskata da labarin?’ Ka yi hankali sa’ad da ka ji jita-jita

KU KALLI BIDIYON NAN TA YAYA ZAN GUJI YAƊA GULMA? SAI KU AMSA WAƊANNAN TAMBAYOYIN:

  • Bisa ga Karin Magana 12:​18, ta yaya kalmominmu za su iya yi wa mutane illa?

  • Ta yaya Filibiyawa 2:4 take taimaka mana mu san abubuwan da ya kamata mu faɗa game da wasu?

  • Me ya kamata mu yi sa’ad da mutane suka soma faɗan abubuwan da ba su dace ba game da wasu?

  • Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu kafin mu soma magana game da wasu?