Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Yin Wa’azi a Gidajen da Akwai Kamara ko Tarho

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Yin Wa’azi a Gidajen da Akwai Kamara ko Tarho

MUHIMMANCINSA: Yadda ake yawan mugunta a yau da kuma ci gaba da ake samuwa a fasaha sun sa mutane suna saka kamarori da kuma tarho a gidajensu. Mai yiwuwa za mu iya jin tsoron yi wa mutanen da ba ma gani wa’azi. Shawara da ke gaba za ta taimaka mana mu yi wa’azi a gidajen da aka saka kamarori ko tarho ba tare da jin tsoro ba.

YADDA ZA MU YI HAKAN:

  • Ka kasance da ra’ayin da ya dace. Mutane da yawa da suka saka kamara ko tarho a gidajensu za su so su tattauna da mu

  • Amma ya kamata mu tuna cewa wasu kamarorin suna soma rikodin kafin mu kwankwasa ƙofar kuma maigidan zai iya gani da kuma jin abin da muke faɗa da zarar mun yi kusa da ƙofar gidan

  • Idan mutumin ya amsa, ka yi magana ta tarhon ko kamarar kamar kana ganinsa. Ka yi fara’a kuma ka yi magana a sake. Ka faɗi ainihin abin da kake so ka gaya masa in da ya fito. Idan akwai kamara a gidan da kake wa’azin, kada ka je kusa da kamarar sosai. Idan mai gidan bai amsa ba, kada ku bar saƙo

  • Bayan ka gama masa wa’azi, kar ka manta cewa maigidan zai riƙa ganinku da kuma jin abin da kuke tattaunawa