Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | YOHANNA 7-8

Yesu Ya Ɗaukaka Ubansa

Yesu Ya Ɗaukaka Ubansa

7:15-18, 28, 29; 8:29

Yesu ya ɗaukaka Ubansa a dukan abubuwan da ya yi da kuma faɗa. Yesu yana son mutane su san cewa koyarwarsa daga wurin Allah ne. Shi ya sa a kowane lokaci, yana ƙaulin nassosi sa’ad da yake koyarwa. Sa’ad aka yaba masa, Yesu ya miƙa godiyar ga Jehobah. Abin da ya fi masa muhimmanci shi ne ya gama aikin da Jehobah ya ba shi.​—Yoh 17:4.

Ta yaya za mu yi koyi da Yesu sa’ad da . . .

  • muke nazari da ɗalibanmu ko kuma muke yin jawabi?

  • wasu suka yaba mana?

  • muke tunanin yadda za mu yi amfani da lokacinmu?