Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwa

Gabatarwa

HASUMIYAR TSARO

Tambaya: Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da mala’iku?

Nassi: Za 103:20

Littafi: Wannan mujallar ta bayyana abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da mala’iku da kuma yadda suke shafan rayuwarmu.

KU KOYAR DA GASKIYA

Tambaya: Kana ganin ilimin kimiyya ya ƙaryata Littafi Mai Tsarki ne?

Nassi: Ish 40:2

Gaskiya: Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce a kan batun kimiyya daidai ne.

TAKARDAR GAYYATA ZUWA TARO (inv)

Littafi: Ina son in gayyace ka ka saurari wani jawabin da za a yi a Majami’ar Mulkinmu. [Ka ba da takardar gayyatar, ka nuna masa lokaci da kuma wurin da ake taron kuma ka ambata jigon jawabin da za a yi a ranar.]

Tambaya: Ka taɓa zuwa Majami’ar Mulki kuwa? [Idan da dama, ka nuna bidiyon nan Me Ake Yi a Majami’ar Mulki?]

KA RUBUTA TAKA GABATARWA

Ku yi amfani da fasalin da ke baya don rubuta taku gabatarwar wa’azi.