Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwa

Gabatarwa

HASUMIYAR TSARO

Tambaya: Muna bukatar ƙarfafa ko kuma ta’aziya a kullum. Amma a ina ne za mu iya samun ta’aziya ko kuma ƙarfafa?

Nassi: 2Ko 1:3, 4

Abin da Za Ka Ce: Wannan Hasumiyar Tsaron ya nuna yadda Allah zai ƙarfafa ko ta’azantar da mu.

HASUMIYAR TSARO (bangon baya)

Tambaya: Wasu suna tunanin cewa Mulkin Allah yana zuciyar mutum; wasu kuma suna ganin cewa ƙoƙarce-ƙoƙarcen ʼyan Adam ne wajen kawo salama a duniya. Mene ne ra’ayinka?

Nassi: Da 2:44

Abin da Za Ka Ce: Littafi Mai Tsarki ya ce Mulkin Allah gwamnati ce ta musamman. Wannan talifin ya tattauna wasu abubuwa da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da Mulkin Allah.

KU KOYAR DA GASKIYA

Tambaya: Ta yaya za mu san cewa Allah yana kula da mu?

Nassi: 1Bi 5:7

Gaskiya: Allah yana son mu yi masa addu’a don yana kula da mu.

KA RUBUTA TAKA GABATARWA

Ku yi amfani da fasalin da ke baya don rubuta taku gabatarwar wa’azi.