Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FITOWA 31-32

Ku Guji Bautar Gumaka

Ku Guji Bautar Gumaka

32:1, 4-6, 9, 10

Da alama daga wurin Masarawa ne Isra’ilawa suka koyi bautar gumaka. A yau, mutane suna bautar gumaka a hanyoyi dabam-dabam, wasunsu ma zai mana wuya mu gane. Ko da yake ba za mu yi bautar gumaka kai tsaye ba, amma za mu iya barin haɗama ta hana mu bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya.

Waɗanne abubuwa nake yi da za su iya janye hankalina daga bautar Jehobah, kuma ta yaya zan guji ɗaukan su da muhimmanci fiye da bautar Jehobah?