Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Matasa​—Jehobah Ne Babban Abokinku?

Matasa​—Jehobah Ne Babban Abokinku?

Waɗanne irin halaye ne kake so abokinka ya kasance da su? Mai yiwuwa kana so ya kasance mai aminci da alheri da kuma bayarwa. Jehobah yana nuna dukan waɗannan halayen. (Fit 34:6; A. M 14:17) Idan ka yi masa addu’a, zai ji ka. Lokacin da kake bukatar taimako, zai taimaka maka. (Za 18:​19, 35) Yana gafarta zunubanka. (1Yo 1:9) Hakan ya nuna cewa Jehobah Abokin ƙwarai ne!

Ta yaya za ka zama abokin Jehobah? Ka koya game da shi ta wajen karanta Kalmarsa. Ka dogara gare shi. (Za 62:8; 142:2) Ka daraja abubuwan da yake darajawa, kamar Ɗansa da Mulkinsa da kuma alkawarinsa game da nan gaba. Ka koya wa mutane game da shi. (M.Sh 32:3) Idan ka ƙulla abota da shi, shi ma zai zama Abokinka har abada.​—Za 73:​25, 26, 28.

KU KALLI BIDIYON NAN MATASA​—‘KU ƊANƊANA KU GA JEHOBAH MAI ALHERI NE,’ SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Ta yaya za ka shirya yin alkawarin bauta ma Jehobah da kuma baftisma?

  • Ta yaya ’yan’uwa a ikilisiya za su taimaka maka ka bauta ma Jehobah?

  • Ta yaya wa’azi yake ƙarfafa dangantakarka da Jehobah?

  • Abota da Jehobah za ta dawwama har abada!

    Wace hidima ce za ka iya yi a ƙungiyar Jehobah?

  • Me ka fi so game da Jehobah?