Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FITOWA 37-38

Bagadai da Ke Mazauni da Amfaninsu a Bauta Ta Gaskiya

Bagadai da Ke Mazauni da Amfaninsu a Bauta Ta Gaskiya

37:25, 29; 38:1

An gina bagadan daidai da yadda Jehobah ya faɗa kuma suna da muhimmanci.

  • Jehobah yana jin daɗin addu’o’in da bayinsa suke masa kamar yadda yake jin daɗin turaren ƙonawa

  • Jehobah yana karɓan hadayun da aka yi a bagaden ƙona hadayu. Yadda aka yi bagaden a gaban mazaunin, ya nuna mana cewa dole ne mu ba da gaskiya ga hadayar Yesu don Jehobah ya amince da mu.​—Yoh 3:​16-18; Ibr 10:​5-10

Ta yaya za mu sa addu’armu ta zama kamar turare mai ƙamshi a gaban Allah?​—Za 141:2