Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Kana Daukan Littafi Mai Tsarki da Daraja Kuwa?

Kana Daukan Littafi Mai Tsarki da Daraja Kuwa?

Jehobah ne Mawallafin Littafi Mai Tsarki, shi ya sa Littafi Mai Tsarki yake koya mana ra’ayin Jehobah game da abubuwa. (2Bi 1:​20, 21) Littafi Mai Tsarki ya nanata yadda Mulkin Allah zai nuna cewa Jehobah ne kaɗai ya cancanci ya yi sarauta kuma ’yan Adam za su ji daɗin rayuwa nan ba da daɗewa ba. Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana halaye masu kyau na Ubanmu Jehobah.​—Za 86:15.

Dukanmu muna da dalilin da ya sa muke ɗaukan Littafi Mai Tsarki da daraja sosai. Amma za mu fi nuna cewa muna daraja shi idan muna karanta da kuma bin shawarwarinsa. Bari ayyukanmu su nuna cewa mun amince da abin da marubucin zabura ya ce: “Ina misalin ƙaunata ga Koyarwarka!”​—Za 119:97.

KU KALLI BIDIYON NAN SUN ƊAUKI LITTAFI MAI TSARKI DA MUHIMMANCI​—GAJEREN BIDIYO NA LABARIN (WILLIAM TYNDALE), SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Me ya sa William Tyndale ya fassara wani sashe na Littafi Mai Tsarki?

  • Me ya sa fassara Littafi Mai Tsarki da Tyndale ya yi ba ƙaramin aiki ba ne?

  • Ta yaya aka kai Littafi Mai Tsarki da Tyndale ya fassara zuwa Ingila?

  • Ta yaya kowannenmu zai nuna cewa yana daraja Littafi Mai Tsarki?