Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Yin Ladabi da Biyayya Yakan Rinjayi Mutane

Yin Ladabi da Biyayya Yakan Rinjayi Mutane

Mata masu bi, sukan rinjayi mazajensu su soma bauta ma Jehobah ta wurin halayensu masu kyau. Amma mace za ta iya yin shekaru da yawa tana jimrewa kafin ta iya yin hakan. (1Bi 2:​21-23; 3:​1, 2) Idan maigidanki yana wulaƙanta ki, ki ci gaba da jimrewa don ki iya rinjayi mugunta da nagarta. (Ro 12:21) Mai yiwuwa maigidanki ba zai saurari wa’azin da kike masa ba, amma idan ya lura da halinki mai kyau, hakan zai iya rinjaye shi ya soma bauta ma Jehobah.

Ki yi iya ƙoƙarinki don ki fahimci maigidanki. (Fib 2:​3, 4) Ki zama mai tausayi kuma ki yi ƙoƙari ki cika duk hakkinki na matan aure. Ki riƙa sauraran sa da kyau. (Yak 1:19) Ki riƙa haƙuri kuma ki tabbatar wa maigidanki cewa kina ƙaunarsa. Ko da maigidanki ba ya daraja ki kamar yadda kike masa, ki tabbata cewa Jehobah yana farin ciki domin amincinki.​—1Bi 2:​19, 20.

KU KALLI BIDIYON NAN JEHOBAH YANA ƘARFAFA MU DON MU JURE WAHALA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Yaya rayuwa ta kasance wa Grace Li jim kaɗan bayan ta yi aure?

  • Me ya sa ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki?

  • Ta yaya ’yar’uwa Li ta jimre da matsaloli bayan ta yi baftisma?

  • Wace addu’a ce ’yar’uwa Li ta yi a madadin maigidanta?

  • Wace albarka ’Yar’uwa Li ta samu domin ta yi ladabi da biyayya?

Ladabi da biyayya suna da muhimmanci sosai!