Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Jehobah Yana Son Mu Kasance da Tsabta

Jehobah Yana Son Mu Kasance da Tsabta

Iyaye da yawa suna koya wa yaransu yadda za su kasance da tsabta. Shi ya sa sukan gaya musu: “Ka wanke hannunka. Ka share ɗakinka. Ka wanke kwano. Ka zubar da datti.” Amma Jehobah ne ainihin wanda ya koya wa dukanmu yadda za mu kasance da tsabta. (Fit 30:​18-20; M.Sh 23:14; 2Ko 7:1) Idan muna tsabtace jikinmu da kayanmu, muna ɗaukaka Jehobah ne. (1Bi 1:​14-16) Gidajenmu da mahallinmu fa? Wasu mutane suna zubar da datti duk inda suka ga dama, amma mu Kiristoci muna iya ƙoƙarinmu wajen tsabtace gidajenmu da mahallinmu. (Za 115:16; R. Yar 11:18) Yadda muke zubar da ledar minti ko gwangwani ko kuma cingam zai nuna ko muna da tsabta ko a’a. Muna so mu yi iya ƙoƙarinmu “mu nuna cewa mu masu hidimar Allah ne” a dukan abubuwan da muke yi.​—2Ko 6:​3, 4.

KU KALLI BIDIYON NAN ALLAH YANA SON MU KASANCE DA TSABTA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Me ya sa wasu suke ƙin tsabtace jikinsu da mahallinsu?

  • Ta yaya Dokar da aka ba da ta hannun Musa ta nuna cewa Jehobah yana son tsabta?

  • Ta yaya za mu ɗaukaka Jehobah a ayyukanmu?

Ta yaya zan nuna cewa ina son tsabta kamar Jehobah?