Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Kauna Ce Alamar Kiristoci na Gaskiya​—Ku Guji Son Kai da Saurin Fushi

Kauna Ce Alamar Kiristoci na Gaskiya​—Ku Guji Son Kai da Saurin Fushi

ME YA SA YAKE DA MUHIMMANCI: Yesu ya ce ƙauna ce za ta sa a san mabiyansa na gaskiya. (Yoh 13:​34, 35) Idan muna so mu ƙaunaci ’yan’uwanmu kamar yadda Kristi ya yi, dole ne mu yi abin da zai faranta musu rai kuma mu guji yin fushi a kowane lokaci.​—1Ko 13:5.

YADDA ZA MU YI HAKAN:

  • Idan wani ya ɓata mana rai, mu tsaya mu yi tunani a kan dalilin da ya sa ya yi hakan da kuma abin da zai iya faruwa idan muka yi magana da fushi.​—K. Ma 19:11

  • Mu tuna cewa dukanmu ajizai ne kuma mukan faɗi ko yi abin da za mu yi da-na-saninsa daga baya

  • Mu riƙa sasanta matsaloli da sauri

KU KALLI BIDIYON NAN “KU KAUNACI JUNA”​—KU GUJI SON KAI DA SAURIN FUSHI, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Mene ne Larry ya yi sa’ad da Tom ya gaya masa wani abu?

  • Ta yaya tunanin da Tom ya yi, ya taimaka masa ya guji saurin fushi?

  • Me ya faru bayan da Tom ya amsa ma Larry a hankali?

Ta yaya ’yan’uwa a ikilisiya za su amfana idan wani ya ɓata mana rai kuma muka kame kanmu?