Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Ka Yabi Jehobah Ta Yadda Kake Rayuwa!

Ka Yabi Jehobah Ta Yadda Kake Rayuwa!

Rai kyauta ne mai tamani daga Allah. Yadda muke bi da rayuwarmu a kullum yana nuna ko mun daraja wannan kyauta ko a’a. A matsayinmu na Shaidun Jehobah, muna yin amfani da baiwarmu don mu girmama Jehobah, wanda ya ba mu rai. (Za 36:9; R. Yoh 4:11) Amma saboda matsaloli na yau da kullum, yana mana wuya mu sa ayyukan ibada farko a rayuwa. (Mk 4:​18, 19) Shi ya sa yake da kyau mu tambayi kanmu: ‘Ina bauta wa Jehobah da dukan ƙarfina kuwa? (Ho 14:⁠2) Aikin da nake yi yana shafan ibadata ga Jehobah? Wane maƙasudi ne na kafa a ibadata? Ta yaya zan faɗaɗa hidimata?’ Idan ka lura cewa kana bukatar ka inganta hidimarka, sai ka yi addu’a ga Jehobah kuma ka yi canji idan da bukata. Babu shakka, bauta wa Jehobah a kullum yana sa mu yi farin ciki a rayuwa!​—⁠Za 61:⁠8.

Wa kake ba wa baiwarka?

KU KALLI BIDIYON NAN KA YI AMFANI DA BAIWARKA A HIDIMAR JEHOBAH, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Me ya sa bai dace mu yi amfani da baiwarmu wajen yi wa duniyar nan hidima ba? (1Yo 2:⁠17)

  • Waɗanne albarka ne waɗanda suke bauta wa Jehobah da dukan ƙarfinsu suke samu?

  • A wace hanya ce za ka iya yin amfani da baiwarka wajen tallafa wa ƙungiyar Jehobah?