Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MISALAI 12-16

Hikima ta Fi Zinariya

Hikima ta Fi Zinariya
DUBA

Me ya sa samun hikimar Allah take da amfani? Tana ceton masu amfani da ita kuma ta sa su ci gaba da rayuwa. Ƙari ga haka, tana kyautata ra’ayinsu da furucinsu da kuma abubuwan da suke yi yau da kullum.

Hikima tana kāre mu daga yin fahariya

16:18, 19

  • Mutum mai hikima yana sanin cewa Jehobah shi ne tushen duk wata hikima

  • Wajibi ne masu gata a ikilisiya su guji fahariya da kuma girman kai

Hikima tana kyautata furucinmu

16:21-24

  • Mai hikima yana amfani da basira wajen sanin halaye masu kyau na mutane kuma ya yaba musu

  • Mai hikima ba ya wa mutane baƙar magana, amma furucinsa suna da daɗi kamar zuma