Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwa

Gabatarwa

AWAKE!

Tambaya: Wasu sun gaskata cewa Yesu ya wanzu, wasu kuma ba su gaskata da hakan ba. Har ila wasu suna shakkar wanzuwarsa. Mene ne ra’ayinka?

Abin da Za Ka Ce: Wannan mujallar Awake! ta tattauna abin da ya tabbatar mana da cewa Yesu ya wanzu da gaske.

KU KOYAR DA GASKIYA

Tambaya: Me yakan faru da mutane sa’ad da suka mutu?

Nassi: Yoh 11:11-14

Gaskiya: Idan mutum ya mutu, ya daina wanzuwa. Don haka, ba ma bukatar jin tsoron abin da zai faru bayan mutuwa. Yesu ya kwatanta mutuwa da barci. Kamar yadda Yesu ya ta da Li’azaru, zai ta da ’yan’uwanmu da abokanmu da suka rasu don su ji daɗin rayuwa a duniya.—Ayu 14:14.

TAKARDAR GAYYATA ZUWA TARO (inv)

Abin da Za Ka Ce: Zan so in gayyace ka don ka saurari wani jawabin Littafi Mai Tsarki kyauta. Za a yi jawabin a Majami’ar Mulki, wato wurin da muke ibada. [Ka ba mutumin takardar gayyatar, bayan haka, ka gaya masa lokaci da kuma wurin da za a yi taron. Kuma ka gaya masa jigon jawabi na makon.]

Tambaya: Ka taɓa zuwa Majami’ar Shaidun Jehobah kuwa? [Idan zai yiwu, ka nuna masa bidiyon nan Me Ake Yi a Majami’ar Mulki?]

KA RUBUTA TAKA GABATARWA

Ku yi amfani da fasalin da ke baya don rubuta taku gabatarwar wa’azi.