LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU Oktoba 2016

Gabatarwa

Yadda za a iya ba da mujallar Awake!, takardar gayyata zuwa taro, da kuma gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki da ta nuna abin da ke faruwa da mu sa’ad da muka mutu. Ka rubuta taka gabatarwar.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

‘Ka Dogara ga Jehobah da Dukan Zuciyarka’

Misalai sura 3 ta tabbatar mana da cewa Jehobah Allah zai albarkace mu idan mun dogara gare shi. Ta yaya za ka nuna cewa ka dogara ga Jehobah da dukan zuciyarka?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

“Kada Ka Bar Zuciyarka ta Karkata”

Misalai sura 7 ta kwatanta yadda wani matashi ya yi zunubi sa’ad da ya daina bin ka’idodin Jehobah. Wane darasi ne za mu iya koya daga misalinsa?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Hikima ta Fi Zinariya

Misalai sura 16 ta ce hikima ta fi zinariya daraja. Me ya sa hikimar da Allah yake tanadarwa take da tamani sosai?

RAYUWAR KIRISTA

Yadda Za Ka Yi Kalami Mai Ratsa Zuciya

Kalamai mai ratsa zuciya tana karfafa mai yin kalamin da kuma ikilisiyar baki daya. Yaya za ka ba da kalami mai ratsa zuciya?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Ku Yi Zaman Lafiya da Mutane

Salamar da bayin Jehobah suke da ita ba ta faruwa haka kawai. Za mu iya yin amfani da Kalmar Allah don sasanta matsaloli kuma mu zauna lafiya.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

“Ka Koya wa Yaro Yadda Zai Yi Zamansa”

Me ya sa ake bukatar yi wa yara horo? Misalai sura 22 tana dauke da shawara mai kyau ga iyaye.

RAYUWAR KIRISTA

Kana Yin Amfani da Katin JW.ORG Yadda Ya Dace Kuwa?

Ka yi amfani da wannan katin a duk inda ka sami zarafi wajen taimaka wa mutane su san Kalmar Allah da kuma dandalin Yanar gizonmu.