Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | LITTAFIN FIRISTOCI 1-3

Manufar Hadayun da Aka Yi

Manufar Hadayun da Aka Yi

1:3; 2:1, 12; 3:1

Dokar alkawari ta bukaci mutane su riƙa ba da hadayu kuma hadayun sun faranta ran Jehobah. Ban da haka ma, hadayun sun yi nuni ga hadayar Yesu ko kuma amfanin hadayar a gare mu. ​—Ibr 8:​3-5; 9:9; 10:​5-10.

  • Kamar yadda aka gaya ma Isra’ilawa su yi hadaya da lafiyayyun dabbobi, haka ma jikin Yesu da ya yi hadaya da shi lafiyayye ne, bai da tabo.​—1Bi 1:​18, 19; ka kalli hoton da ke shafin farko

  • Kamar yadda ake ba da hadayun ƙonawa gaba ɗaya ga Jehobah, haka ma Yesu ya ba da kansa dungum ga Jehobah

  • Kamar yadda Isra’ilawa suke ba da hadayun gyara zumunci don suna da dangantaka mai kyau da Allah, haka ma shafaffu da suke cin gurasa da shan ruwan inabi a Taron Tunawa da Mutuwar Yesu suna da dangantaka mai kyau da Allah