Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

2-8 ga Nuwamba

FITOWA 39-40

2-8 ga Nuwamba

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

 • Musa Ya Bi Umurnin da Aka Ba Shi Daidai”: (minti 10)

  • Fit 39:32​—Musa ya bi umurnin da Jehobah ya ba shi game da ginin mazaunin daidai (w11 9/15 27 sakin layi na 13)

  • Fit 39:43​—Bayan da aka gama ginin mazaunin, Musa da kansa ya je don ya tabbatar ko ginin ya yi daidai

  • Fit 40:​1, 2, 16​—Musa ya kafa mazaunin daidai yadda Jehobah ya gaya masa ya yi (w05 8/1 13 sakin layi na 3)

 • Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 10)

  • Fit 39:34​—Me ya nuna yadda Isra’ilawa suka samo fatun da aka rufe mazaunin da shi? (it-2-E 884 ¶3)

  • Fit 40:34​—Idan ƙunshin girgije ya soma rufe tentin saduwa, me hakan yake nufi? (w15 7/15 21 sakin layi na 1)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da wa’azi da dai sauransu?

 • Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Fit 39:​1-21 (th darasi na 5)

KA YI WA’AZI DA ƘWAZO

 • Bidiyon Haɗuwa ta Fari: (minti 4) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon. Ku dakatar da bidiyon a duk inda bidiyon ya tsaya don ku tattauna tambayoyin da ke bidiyon. Ku tattauna yadda za ku ƙi saka baki a batun siyasa ko wani batu da ake mahawara a kai a yankinku idan maigidan ya tayar da batun.

 • Haɗuwa ta Fari: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka soma da bin bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Ka nuna yadda za ka ba da amsa idan maigidan yana so ya san ra’ayinka game da wani ɗan takarar siyasa ko wani batu makamancinsa. (th darasi na 12)

 • Jawabi: (minti 5 ko ƙasa da hakan) w16.04 23 sakin layi na 8-10​—Jigo: Ta Yaya Za Mu Ƙi Siyasa ko Wani Abu Makamancinsa a Tunaninmu da Kuma Sa’ad da Muke Hira? (th darasi na 14)

RAYUWAR KIRISTA

 • Waƙa ta 123

 • Ka Saurara don Ka Fahimta (Mt 13:16): (minti 15) Ku kalli bidiyon. Sai ka yi waɗannan tambayoyi: Me ya sa muke bukatar mu riƙa saurara sosai don mu fahimci abin da ake faɗa? Mene ne manufar abin da aka faɗa a Markus 4:​23, 24? Da me za mu kwatanta abin da aka faɗa a Ibraniyawa 2:1? Ta yaya za mu nuna cewa muna saurara da kyau don mu fahimta?

 • Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30 ko ƙasa da hakan) ia babi na 20 sakin layi na 14-26 da Taƙaitawa da ke shafi na 179

 • Kammalawa (minti 3 ko ƙasa da hakan)

 • Waƙa ta 139 da Addu’a